Makaratun Faransa Sun Kori Dalibai Kusan 300 Kan Karya Dokar Hana Sanya Hijabi
- Wasu makarantu a kasar Faransa sun kori dalibai da dama da su ka ki bin dokar kasar a jiya Litinin
- Faransa ta kafa dokar sanya hijabi ko abaya a makarantu da duk wani tufafin da ke nuna alamun addini
- Ministan ilimi a kasar, Gabriel Attal shi ya bayyana haka inda ya ce daliban sun bijirewa dokar kasar da ta kafa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Paris, Faransa – Hukumomi a kasar Faransa sun kori wasu dalibai da su ka ki bin dokar hana sanya hijabi a makarantu.
Wannan na zuwa ne ranar farko bayan kasar ta saka dokar sanya abaya da hijabi a makarantu wanda ya jawo cece-kuce a fadin duniya.
Wane mataki Faransa ta dauka kan sanya hijabi?
Ministan ilimi a kasar, Gabriel Attal ya bayyanawa manema labarai cewa dalibai akalla 300 ne su ka ki bin dokar a ranar Litinin 4 ga watan Satumba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce mafi yawancinsu sun sauya tufafin da ke jikinsu sai dai kusan 70 sun ki cire abayan wanda tuni an kore su gida, cewar VOA.
Idan ba a mantaba a watan Agusta ne kasar ta haramta sanya abaya inda ta tabbatar cewa Faransa ba ruwanta da addini.
An yi ta martani a kasashen duniya yayin da wasu ke ganin hakan take hakkin addini ne na mata.
Wane sako Faransa ta tura ga iyaye kan hijabi?
Ministan ya kara da cewa sun bai wa daliban wasiku su kai wa iyayensu inda su ke kara tabbatar da cewa matakin raba addini da lamuran hukuma ba tarnaki ba ne.
Yayin da ya ce idan su ka sake zuwa makarantun a haka, za a sake sabuwar tattaunawa.
Shugaba kasar Faransa, Emmanuel Macron a ranar Litinin 4 ga watan Satumba ya kare matakin wanda ya jawo kace-nace.
Ya ce mutane da dama na kalubalantar matakin Faransa na raba addini da lamuran hukuma inda ya ce irin su ne su ka kashe wani malamin makaranta, Samuel Paty a baya, Gulf News ta tattaro.
Wata kungiyar Musulmai ta shigar da gwamnatin Faransa kara a gaban kotu kan wannan mataki da ta dauka.
An kafa wata doka a Faransa a shekarar 2004 inda ta haramta sanya tufafi ga dalibai da ke nuna alamun addini a makarantu.
Faransa Ta Hana Sanya Hijabi A Makarantu
A wani labarin, Faransa ta sanya dokar hana dalibai sanya hijabi a makarantun kasar gaba daya.
Gabriel Attal, ministan ilmi na Faransa ya bayyana hijabi a matsayin wata alamar addini ce wacce take kawo barazana ga tsarin kafa makarantu.
Asali: Legit.ng