Birnin New York Ta Bai Wa Musulmai Damar Kiran Sallah Ranar Juma'a Da Watan Ramadan
- A karshe al’ummar Musulmai za su samu su sarara bayan birnin New York ta ba su daman kirar salla a wasu zababbun lokuta a birnin baki daya
- Magajin birnin New York, Eric Adams shi ya sanar da haka yayin ganawa da al’ummar Musulmai kan matsalar kiran salla a birnin
- Sanarwar ta ba wa al’ummar Musulmai damar kiran salla a masallatai a ranar Juma’a da kuma watan Ramadan ba tare da neman izini ba
New York, Amurka - Birnin New York a Amurka ta ba da umarnin jiyar da kiran salla a wasu zababbun lokuta a masallatai na birnin baki daya.
Magajin birnin New York, Eric Adams shi ya bayyana haka a ranar Talata 29 ga watan Agusta inda ya ce hakan zai saka Musulmai su ji ana damawa da su.
Meye dokar ta ce kan kiran sallar Musulmai?
A sabuwar dokar, Adams ya ce za a jiyar da kiran sallah ba tare da Musulmai sun nemi izini ba daga hukumomi a ranakun Juma’a da kuma lokacin shan ruwa a watan Ramadan, cewar CNN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sanda za su yi aiki tare da masallatai don bin ka’idojin da aka tsara don tabbatar da karar lasifikan ya yi dai-dai da tsari.
Adams wanda ya ke tare da shugabannin Musulman birnin New York ya ce:
“Musulman birnin New York za su samu sararawa a matsayina na magajin birnin.”
Meye dalilin daukar matakin kiran sallar Musumai?
AP News ta tattaro Adams na cewa:
“An dauki tsawon lokaci ana samun rikitarwa a kan wadanne yankuna ne ba a barin a yi kiran sallah da lasifika.
Jaruma Lizzy Anjorin Ta Bar Musulunci, Ta Yi Gargadi Mai Tsauri a Bidiyo: "Ba Musulmin Da Ya Kare Ni Lokacin Da Ake Tsangwamata"
“A yau muna so mu kawo karshen wannan abu inda muke bayyana cewa masallatai na iya yin kiran sallah a bayyane a ranakun Juma’a da kuma watan Ramadan ba tare da sake neman izini ba,”
Indiya Ta Rufe Makaranatar Da Aka Ci Zarafin Dalibi Musulmi
A wani labarin, yayin da ake ta cece-kuce bayan ganin wani faifan bidiyo da wata malama ke cin zarafin dalibi Musulmi, hukumomi sun dauki mataki.
Hukumomi a kasar Indiya sun rufe makarantar da aka samu wannan cin zarafi tare da gurfanar da malamar don amsa tambayoyi.
Asali: Legit.ng