Wata Mata Ta Haifi Yara 9 Cikin Shekaru 13, Ta Ce Saura Na Nan Tafe
- Tun bayan da Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong suka yi aure, suna haihuwar sabon 'da duk shekara
- Sun yi sauki ne a 2020 lokacin da annoba ta barke kafin suka koma bakin aiki bayan abubuwa sun koma daidai
- Masoyan wadanda ke ganiyar shekaru 30 da doriya suna da yara tara a yanzu haka, suna tsammanin haihuwar na 10 kuma basu shirya dakatawa nan kusa ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata yar kasar China mai suna Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong sun ja hankalin jama'a bayan sun haifi yara tara a cikin shekaru 13 da suka gabata.
A cewar Mothership, matar wacce ke ganiyar shekaru 30 da doriya ta haifi diyarta ta farko a 2010.
Sun fara soyayya a makaranta
Da aka tambayeta kan dalilin da yasa take haihuwa ba kakkautawa, ta bayyana cewa bata so ta "yi asarar kwayoyin halittar mijinta."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta ci gaba da bayanin cewa hikimarta shine ci gaba da haihuwar yara har sai ta kai 12 don kowani yaro ya wakilci 'ilimin taurari' na kasar China.
"Na fada tarkon son Tian a ganin farko da nayi mata lokacin muna babbar makaransa sannan na fara bibiyarta har sai da ta yarda ta so ni," Zhao ya bayyana.
A 2012, shekaru biyu bayan Tian ta haifi diyarsu ta farko, sai Allah ya azurta ma'auratan da haihuwar yan biyu maza.
Sun yi sauki saboda annoba
Bayan su haifi yara uku, Tian da Zhao sun ga cewa lokaci ya yi da za su dakata, amma Tian tace ta ji tana son haihuwar karin yara domin gidan ya zama cikin walwala.
Wannan ne yasa a 2016, ma'auratan suka sake haihuwar diya mace wacce ta zama ta hudu.
A shekaru hudu da suka biyo baya, ma'auratan sun sake haihuwar yara hudu inda gaba daya suka zama takwas har sai da annoba ta kunno kai sannan suka jinkirta.
Da abubuwa suka daidaita, masoyan sun sake haihuwa a 2022 inda yaran suka zama tara a yanzu.
Suna tsammanin 'da na 10
A daidai lokacin kawo wannan labarin, Tian ta yi nauyi tana dauke da juna biyu inda ma'auratan ke tsammanin 'da na 10 kuma suna da burin kara wasu.
A cewarta, tana da niyan ci gaba da haihuwa har sai gidan an samu yaran sun cika 'ilimin taurari' na kasar China. Duba ga haka, yanzu akalla sai ta haigfi yara biyar a nan gaba.
Yadda matashiya ta kona gaba daya kayanta masu nuna tsaraici
A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta saki bidiyo da ke nuna lokacin da ta kona gaba daya kaya masu nuna tsaraici da ta mallaka.
A bidiyon da aka wallafa a ranar Asabar, 27 ga watan Agusta, Precious Thamani ta ce ta yanke shawarar zama kirista ta gaske.
Asali: Legit.ng