Shugaba Biden Ya Zargi Putin Da Hannu A Kisan Shugaban Sojin Wagner, Prigozhin

Shugaba Biden Ya Zargi Putin Da Hannu A Kisan Shugaban Sojin Wagner, Prigozhin

  • Joe Biden, shugaban kasar Amurka ya zargi Vladimir Putin na Rasha da hannu a cikin kisan shugaban sojin Wagner, Yevgeny Prigozhin
  • Biden ya ce ko kadan bai yi mamaki ba da mutuwar Yevgeny saboda ya sani kusan komai a Rasha Putin na da hannu a ciki
  • A jiya Laraba ne 23 ga watan Agusta, shugaban sojin Wagner da wasu mutum 10 su ka mutu a hadarin jirgin sama

Washington, Amurka – Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya zargi shugaban Rasha Vladimir Putin kan kisan Yevgeny Prigozhin.

Biden ya ce bai yi mamaki ba ganin yadda shugaban Rasha bai ce komai ba game da faduwar jirgin da ya yi sanadin mutuwar shugaban sojin haya na Wagner.

Joe Biden ya zargin Shugaba Putin da hannu a kisan shugaban sojin Wagner, Prigozhin
Shugaba Biden Na Amurka Ya Zargi Putin Na Rasha Da Kisan Shugaban Sojin Wagner, Prigozhin. Hoto: BBC.
Asali: Facebook

Meye Biden ke zargin Putin a kai?

Ya ce ya na da tabbacin sa hannun Putin a mutuwar yayin da Yevgeny da wasu su ka yi hatsari a jirgin tare da rasa rayukansu, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Ana Rigima a Kan Kujerar Minista 1 Da Ta Ragewa Bola Tinubu Ya Nada a Gwamnati

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Biden ya yi martani yayin da ya ke amsa tambayoyi daga ‘yan jairdu, ya ce:

“A gaskiya ban san meye ya faru ba amma banyi mamaki ba.
“Ba ko wani abu ba ne daya faru a Rasha da shugaba Putin ba shi da hannu a ciki, amma ban san gaskiyar sosai ba da zan iya ba da amsa.”

Meye Putin ya ce game da kisan Prigozhin?

Hukumomi a kasar Ukraine sun bayyana wannan mutuwar a matsayin gargadi ga manyan kasar Rasha yayin da ake jimamin mutuwar Yevgeny Prigozhin.

Shugaba Putin na Rasha bai ce komai ba game da mutuwar Prigozhin duk da cewa hukumar kula da jiragen sama ta kasar ta yi martani.

Hukumar kula da jiragen sama ta Rasha, Rosaviatsia ta ce Prigozhin da babban kwamandan sojojin Wagner, Dmitry Utkin na daga cikin mutane goma da su ka mutu a hadarin jirgin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaban Sojojin Wagner Tare da Wasu Mutane 9 Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Sama

Ba a bayyana ainihin daliin hatsarin jirgin ba daya fadi a jiya Laraba 23 ga watan Agusta amma rikicin da ke tsakaninsu da Rasha na iya zama hujja, cewar BBC.

Shugaban Sojojin Wagner Ya Mutu A Hatsarin Jirgin Sama A Rasha

A wani labarin, Shugaban rundunar sojojin Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya rasa rayuwarsa a wani hadarin jirgin sama da ya rutsa da shi.

Rahotanni sun tabbatar cewa mutum 10 ne a cikin jirgin sama na haya wanda ya yi hadari a Arewacin Moscow, babban birnin kasar Rasha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.