“Masallacin Maryam, Mahaifiyar Isa”, Kayatattun Hotunan Masallaci Da Aka Canjawa Suna a Dubai

“Masallacin Maryam, Mahaifiyar Isa”, Kayatattun Hotunan Masallaci Da Aka Canjawa Suna a Dubai

  • An canjawa wani katafaren masallaci suna zuwa Maryam, mahaifiyar Isa A.S a Dubai
  • Yariman Birnin Abu Dhabi, Sheikh Mohammad bin Zayed ne ya ba da umarnin sauya sunan
  • Mabiya addinin Kirista da dama sun nuna matuƙar farin cikinsu da wannan gagarumin aiki da aka yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abu Dhabi, UAE - An canjawa wani masallaci suna zuwa Maryam, mahaifiyar Isa A.S daga sunansa na da ‘Sheikh Mohammad Bin Zayed Mosque’ a yankin Al Mushrif, da ke Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Yariman birnin na Abu Dhabi, Sheikh Mohammad bin Zayed Al-Nahyan ne ya ba da umarnin a sauyawa masallacin suna zuwa ‘Mary The Mother Of Jesus Mosque’ kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Hotunan Masallacin Da Aka Sauya Sunansa Zuwa Maryam Mahaifiyar Isa a Dubai
An sauya sunan masallaci zuwa 'Maryam, Mahaifiyar Isa' a Dubai, Hotunan sun bayyana. Hoto: Photo Credit:@Wizillden
Asali: UGC

Dalilin canjawa masallacin suna

Sheikh Mohammad bin Zayed ya ba da umarnin canja sunan Masallacin ne domin inganta kyakkyawar alaƙa tsakanin mabiyan addinan yankin da ke rayuwa a tare.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Yi Martani Bayan Tinubu Ya Rantsar Da Wike a Matsayin Ministan Abuja

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Reverend Canon Andrew Thompson, wanda shi ne babban malami a wata coci da ke kusa da masallacin da aka canjawa sunan, ya nuna matuƙar jin daɗinsa dangane da hakan da aka yi.

Ya bayyana cewa hakan abin farin ciki ne saboda yadda duka manyan addinai biyu ke daraja sunan na mahaifiyar Isa ɗan Maryama amincin Allah ya tabbata a garesu baki ɗaya.

MURIC ta ɗauki zafi kan sanyawa masallaci sunan gwamna Kirista a Oyo

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan zafin da ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC), ta ɗauka dangane da labarin sauya sunan wani masallaci zuwa sunan gwamnan jihar Oyo da ya kasance Kirista.

Ƙungiyar MURIC ta buƙaci a mayar da sunan da masallacin yake da shi a baya saɓanin ma gwamnan da aka sanya a lokacin.

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

Hakan ya biyo bayan sanyawa da gwamnan ya yi a rushe masallacin domin a sake gina shi baki ɗaya da ya yi kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An mayar da coci zuwa Masallaci a ƙasar Turkiyya

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata katafariyar coci da aka mayar da ita masallaci a ƙasar Turkiyya.

Hakan ta ya faru ne a jajiberin ranar Kirsimeti, a wani yanki da ke kusa da Istanbul babban birnin ƙasar ta Turkiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng