Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Ta'adda 40 a Kasar Burkina Faso
- Jami'an 'yan sanda na musamman, sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda 40 a ƙasar Burkina Faso
- Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar
- A yayin arangamar da ta faru tsakanin 'yan ta'addan da jami'an tsaron, 'yan sanda biyar sun rasa rayukansu
Burkina Faso - Jami'an 'yan sanda a ƙasar Burkina Faso, sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 40 a wata arangama da ta faru a tsakaninsu.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar, a yankin Koulpelogo da ke Arewa maso Gabashin ƙasar, yayin da 'yan ta'addan suka yi wa jami'an 'yan sanda na musamman da ke bakin aiki kwanton ɓauna.
'Yan sanda biyar sun rasa ransu yayin gwabzawa da 'yan ta'adda
'Yan sanda biyar sun rasa ransu yayin arangama da 'yan ta'addan a ranar Asabar, 19 ga watan Agustan da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai a yayin arangamar, 'yan ta'addan sun kashe jami'an 'yan sanda biyar kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.
Ƙasashen Burkina Faso, Mali da jamhuriyar Nijar na daga cikin ƙasashen yankin Sahel da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda masu íƙirarin jihadi na tsawon shekaru.
Wasu daga cikin kungiyoyin 'yan ta'addan yankin na da alaƙa da manyan ƙungiyoyin 'yan ta'adda na duniya da suka haɗa da Al-Qaeda da IS kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.
Mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da wasu kuma suka rasa muhallansu daga hare-haren 'yan ta'adda a ƙasashen uku da sojoji ke jagoranta.
'Yan sanda sun dakile harin 'yan ta'adda a Katsina
A baya Legit.ng ta yi wani rahoto kan wani mummunan harin 'yan ta'adda da jami'an 'yan sanda suka daƙile a ƙaramar hukumar Jibia da ke jiha Katsina.
A yayin fafatawar a tsakaninsu da 'yan ta'addan, jami'an 'yan sandan sun yi nasarar halaka ɗan ta'adda ɗay tare da ƙwato makamai da dabbobi masu tarin yawa.
'Yan bindiga sun dauke kansila da wasu mutane 2 a Kaduna
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sace wani kansila a anguwar Mai Taro da ke ƙaramar hukumar Sabo ta jihar Kaduna da 'yan bindiga suka yi.
Haka nan 'yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wata mata a yayin satar kansilan, tare da wani mutum a anguwar Dankande da ke ƙaramar hukumar ta Sabo a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Asali: Legit.ng