Kaduna: Jami'an tsaro sun kai wa 'yan bindiga harin kwanton bauna, sun kashe bakwai
- 'Yan bindiga sun sha mamaki a wurin wasu jami'an tsaro da suka kai musu harin kwanton bauna
- Jami'an tsaro sun dana tarko bayan samun bayanan sirri akan al'amuran 'yan ta'addar yayin da suka fito ofireshon
- An samu gawar biyu daga cikin 'yan bindigar bayan an tsagaita musayar wuta a tsakani
A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa rundunar jami'an tsaro ta 'Thunder Srike' ta kaddamar da harin kwanton bauna akan wasu 'yan bindiga a yankin karamar hukumar Kagarko.
Mista Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, ya sanar da cewa jami'an tsaro sun kashe biyu daga cikin 'yan bindigar a cikin jawabin da ya fitar.
A cewar Aruwan, rundunar jami'an tsaro ta samu nasarar kaddamar da harin ne a daren ranar Litinin a kan hanyar Sabon Iche zuwa Kagarko, kamar yadda Leadership ta wallafa.
"Sun fito neman wurin da zasu fara ta'addancinsu a yayin da su kuma jami'an tsaro suka labe a wata kwana suna jiran karasowarsu.
KARANTA: Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka
"Sun fada tarkon jami'an tsaron wadanda suka bude musu wuta nan take. Sai dai, 'yan bindigar sun mayar da martani nan da nan.
KARANTA: Ban yarda da ita ba; Yahaya Bello ya gargadi 'yan Nigeria akan rigakafin Korona
"An samu gawar biyu daga cikin 'yan bindigar bayan tsagaitawar musayar wuta a yayin da ake zargin sauran sun tsere zuwa cikin daji da raunukan bindiga.
"Babu asarar rai ko samun rauni a bangaren rundunar jami'an tsaro" a cewarsa.
Legit.ng ta rawaito cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun kai samame tare da cafke wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da mutane.
Daga cikin mutanen hudu har da wata mace da ak kashe mijinta a cikin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Matar ta shiga sana'ar garkuwa da mutane bayan an kashe mijinta, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng