Juyin Mulkin Nijar: Janar Tchiani Ya Amince Zai Tattauna Da ECOWAS

Juyin Mulkin Nijar: Janar Tchiani Ya Amince Zai Tattauna Da ECOWAS

  • Bayan kwashe dogon lokaci ana neman hanyar mafita dangane da juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, daga ƙarshe an samu ƙofar yin sulhu
  • Shugaban juyin mulkin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya amince zai tattauna da ƙungiyar ECOWAS domin samo mafita
  • Firaministan ƙasar shi ne ya bayyana hakan inda ya nuna fatansa kan cewa tattaunawar za ta wakana a cikin ƴan kwanaki masu zuwa

Jamhuriyar Nijar - Shugaban juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya amince ya hau teburin sulhu da hukumar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS).

Janar Tchiani ya amince ya tattauna da ƙungiyar ECOWAS ne bayan ya gana da tawagar malaman addinin musulunci a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, a Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar Sun Fadi Mummunan Abinda Zai Samu Najeriya Da Ba Su Yi Juyin Mulki Ba

Janar Tchiani ya amince zai tattauna da ECOWAS
Janar Abdourahamane Tchiani ya amince zai tattauna da ECOWAS Hoto: RTN-EFE
Asali: Getty Images

A cewar rahoton Zagazola Makama, Firaministan Jamhuriyar Nijar shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Nan ba da jimawa ba za a hau teburin sulhu

Firaministan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, Janar Tchiani ya bayar da ƙofar tattaunawa da ECOWAS, inda ya nuna fatansa cewa tattaunawar za ta wakana a cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lamine Zaine ya bayyana cewa suna fatan a tatttaunawar da za a yi, ƙungiyar ECOWAS za ta janye jerin takunkumin da ta ƙaƙabawa ƙasar tun bayan da sojojin suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, a watan da ya gabata.

"Mun amince sannan shugaban ƙasar mu ya bayar da kafar da za a hau teburin sulhu. Yanzu za su koma su gaya wa shugaban ƙasar Najeriya cewa sun ji daga gare mu... Muna fatan cewa a cikin ƴan kwanaki masu zuwa, wakilan ECOWAS za su zo nan su same mu domin tattauna yadda za a janye takunkumin da aka ƙaƙaba mana." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Nijar: Manyan Matakan ECOWAS 4 Da Suke Neman Janyowa Bazoum Matsala Daga Sojojin Juyin Mulki

Malaman Najeriya Sun Magantu Bayan Zuwa Jamhuriyar Nijar

A wani labarin kuma, malaman Najeriya da suka kai ziyara Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa da Janar Tchiani, sun bayyana yadda tattaunawarsu ta kaya.

Malaman addinin a ƙarƙarshin jagorancin Abdullahi Bala Lau, sun bayyana cewa sun samu nasara a tattaunawar da suka yi da sojojin da suka kifar da gwamnati a ƙasar ta Jamhuriyar Nijar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng