Juyin Mulkin Nijar: Peter Obi Ya Bayyana Abun da Ya Kamata ECOWAS Ta Yi

Juyin Mulkin Nijar: Peter Obi Ya Bayyana Abun da Ya Kamata ECOWAS Ta Yi

  • Peter Obi ya ba kungiyar ECOWAS shawarwari kan yadda za ta shawo kan rikicin da ke faruwa a jamhuriyar Nijar
  • Obi ya ce ya kamata ECOWAS ta yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen magance rikicin bayan sojoji sun karbe mulkin kasar
  • Tawagar malaman Najeriya sun tattauna da sojojin juyin mulkin Nijar a wani mataki na hana zubar jini

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party( LP), Peter Obi, ya bayyana abun da ya kamata kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi game da rikicin da ke gudana a Jamhuriyar Nijar bayan sojoji sun yi juyin mulki.

Obi ya ce lamarin Nijar batu ne mai zafi ga kungiyar ECOWAS kuma ya kamata a yi amfani da tattaunawa da diflomasiyya wajen magance rikicin.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Majalisar ECOWAS ta dare kan lamarin Nijar, bayanai sun bayyana

Peter Obi ya ce ECOWAS ta nemi tattaunawa da sojojin juyin mulki a Nijar
Juyin Mulkin Nijar: Peter Obi Ya Bayyana Abun da Ya Kamata ECOWAS Ta Yi Hoto: Mr Peter Obi/@BashirAhmaad
Asali: UGC

Dole ne ECOWAS ta yi amfani da tattaunawa da diflomasiyya don warware rikicin Nijar

"Shakka babu, lamarin Nijar batu ne mai zafi ga kungiyar ECOWAS, da ma sauran masu shiga tsakani na kasa da kasa, ba tare da la'akari da matsayin bangarori daban-daban da ke da muradin kai tsaye ko na zahiri ba a Nijar, dole ne a karfafa tattaunawa da diflomasiyya wajen cimma matsaya wanda ba zai kawo illa sosai ga Najeriya da yankin yammacin Afirka ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dole a yi la'akari da matakin daiflomasiyya na siyasar gaskiya a yankin na yammacin Afrika."

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter @PeterObi, ya ce ya zama dole diflomasiyya ta ci gaba da kasancewa kan gaba a cikin hanyoyin magance rikice-rikice da ECOWAS ke da su.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Ya yaba ma kokarin shiga tsakani da Janar Abdulsalami Abubakar, Mai girma Muhammadu Sa'ad Abubakar, sarkin Musulmi da mai martaba Sanusi Lamido Sanusi, suka yi don kawo maslaha ga rikicin.

Malaman Najeriya sun tattauna da shugabannin sojojin Nijar

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa malaman addinin Musulunci a Najeriya sun samu damar zantawa da sojojin juyin mulki a Janhuriyar Nijar yayin da ake ci gaba da takkadama tsakaninsu da kungiyar ECOWAS.

Malaman Najeriya sun ajiye banbancin hakida sun hada kai zuwa Nijar a kokarin da suke na ganin an samu maslaha tare da hana zubar jini a kasar ta yammacin Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng