Juyin Mulki: Sanusi Ya Yi Bayanin Ganawarsa Da Tinubu Bayan Ziyarar Sulhu Da Ya Kai Nijar

Juyin Mulki: Sanusi Ya Yi Bayanin Ganawarsa Da Tinubu Bayan Ziyarar Sulhu Da Ya Kai Nijar

  • Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana dalilin da ya sa ya ziyarci fadar shugaban kasa bayan ya dawo daga Nijar
  • Ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne domin yiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayanin sakamakon ganawarsa da gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar
  • Sai dai Sanusi bai bayyana ko ziyarar tasa ta cimma nasara ba, amma ya ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa don samar da zaman lafiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, ya yi wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayani game da ziyarar da ya kai Jamhuriyar Nijar a wani mataki na shiga tsakani da samar da zaman lafiya tare da mayar da kasar ta yammacin Afrika kan tsarin dimokradiyya.

A ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, ne Sanusi ya gana da shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar a kokarin yin sulhu da sakin hambararran shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da iyalinsa, wadanda aka tsare tun bayan juyin mulki a ranar Laraba, 29 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Sanusi ya korowa Tinubu bayani kan ziyarar sulhu da ya kai Nijar
Juyin Mulki: Sanusi Ya Yi Bayanin Ganawarsa Da Tinubu Bayan Ziyarar Sulhu Da Ya Kai Nijar Hoto: @BMB1_Official
Asali: Twitter

Kamar yadda Arise TV ta rahoto, Sanusi ya bar Yamai, babban birnin kasar Nijar, zuwa Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya don ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Da manema labarai suka tambaye shi game da dalilin ganawarsa da shugaban kasar, Sanusi ya amsa, yana mai cewa ya ziyarci fadar villa ne don yi wa Shugaban kasa Tinubu bayani game da ganawarsa da shugabannin juyin mulki a Nijar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Eh na zo ne don yi masa (Tinubu) bayani kan tattaunawata da shugabannin Nijar."

Sanusi yana da yakinin za a samu maslaha ta gaggawa

Da aka tambaye shi ko tsoma bakinsa ya cimma nasara da shugabannin sojin Nijar, Sanusi ya ce:

"Ana ci gaba da shiga tsakani, kuma za mu ci gaba da yin iyakacin bakin kokarinmu wajen hada bangarorin biyu domin inganta fahimtar juna. Wannan lokaci ne na diflomasiyya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Bayan Ganawa Da Shugabannin Juyin Mulkin Nijar, Sanusi Na Kus-Kus Da Tinubu

"Ba abu ne da za mu bar wa gwamnatoci ba. Akwai bukatar gaba daya yan Najeriya, gaba daya yan Nijar su shiga lamarin domin samun maslaha da za ta yi aiki ga Afrika, maslaha da za ta yi aiki ga Nijar, wanda za ta yi aiki ga Najeriya da kuma maslaha da za ta yi aiki ga yan adam."

A halin da ake ciki, Sanusi ya bayyana cewa ba gwamnatin tarayya bace ta dauki nauyin ziyarar da ya kai Jamhuriyar Nijar.

Ya ce ya ziyarci Nijar ne bisa gashin kansa a matsayinsa na jagora wanda ke son zaman lafiya da hadin kai a tsakin kasashe. Sai dai, Sanusi ya bayyana cewa gwamnati na sane da ziyarar tasa.

Gwamnatin sojan Nijar ta ki ganawa da wakilan Amurka

A baya mun ji cewa gwamnatin sojin kasar ta ki amincewa da wani taron da aka shirya yi da wakilan kungiyar Tarayyar Afirka (AU), kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), da kuma jami'an diflomasiyya na Amurka.

Hankalin duniya gaba daya ya karkata kan Nijar bayan juyin mulki da aka yi a kasar wanda ya girgiza yankin a yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng