Tsohon Shugaban Yan Tawayen Nijar Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Don Yakar Masu Juyin Mulki
- Tsohon shugaban yan tawaye kuma dan siyasar Nijar, Rhissa Ag Boula, ya kafa wata kungiya domin adawa da masu juyin mulki a kasar
- Kungiyar mai suna Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya (CRR) tana da kudirin mayar da hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum kan mulki
- A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli ne gwamnatin soja ta kwace mulki daga hannun Bazoum, ta hanyar juyin mulkin da ba a taba ganin irinsa ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jamhuriyar Nijar - Hankula sun kara tashi a jamhuriyar Nijar bayan wani tsohon shugaban yan tawaye kuma dan siyasa, Rhissa Ag Boula, ya kaddamar da wata kungiya domin adawa da masu juyin mulki, wadanda suka hambarar da Shugaban kasa Mohamed Bazoum daga karagar mulki.
Kamar yadda VOA ta rahoto, Boula a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce sunan kungiyar Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya wato Council of the Resistance for the Republic (CRR).
Nijar Ta Nada Shirgegen Mukami Yayin Da Kasar Ke Cikin Matsin Lamba Na Mika Mulki Daga ECOWAS, Bayanai Sun Fito
Tsohon shugaban yan tawayen Nijar ya kaddamar da kungiya don tunkarar masu juyin mulki
Ya ce an kafa kungiyar ne domin dawo da Bazoum a matsayin shugaban kasar Jamhuriyar Nijar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Boula ya kasance tsohon ministan yawon bude ido kuma jigo a rikicin kabilanci Abzinawa guda biyu a Nijar, daya a shekarun 1990, daya kuma daga 2007 zuwa 2009.
Mun dai ji cewa sojojin da suka yi juyin mulki sun tsare Idrissa Kane a Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.
Idrissa Kane da ne ga Aïchatou Boulama Kané, hambarrariyar jakadar Nijar a Faransa wacce ta yi mubaya'a ga hambararre kuma tsararren Shugaba Mohamed Bazoum.
Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Zauna da Sojojin da Su ka Kifar da Bazoum a Nijar
A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya sa labule da Shugaban sojojin tawayen Jamhuriyar Nijar, Janar Abdulrahmane Tchiani.
Hotunan da mu ka samu daga kafofin sadarwa na zamani sun tabbatar da cewa Sarkin Kano na 14 ya yi zama da sojojin da su ka karbe iko a Nijar.
An tattaro cewa an yi taron ne a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, a Yamai watau Niamey, babban birnin Nijar a lokacin da abubuwa su ke faman canza zani.
Asali: Legit.ng