Zakzaky Ya Fito da Sirrin Rikicin Nijar, Ya ba Bola Tinubu Muhimiyyar Shawara

Zakzaky Ya Fito da Sirrin Rikicin Nijar, Ya ba Bola Tinubu Muhimiyyar Shawara

  • Ibraheem El-Zakzaky ya bayyana cewa kusan jirgi daya ya dauko mutanen Nijar da na Najeriya
  • Shugaban Islamic Movement of Nigeria (IMN) ya ja-kunne a kan shirin aukawa makwabta da yaki
  • El-Zakzaky ya na da ra’ayin cewa Amurkawa da Faransawa ne su ke so a yaki Jamhuriyyar Nijar

Abuja - Jagoran kungiyar IMN a Najeriya, Ibraheem El-Zakzaky ya gargadi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu game da shiga kasar Nijar da fada.

Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya yi wannan kira ne a lokacin da wasu makarantan Al-Kur’ani su ka kai masa ziyara, Tribune ta fitar da rahoton a jiya.

A yayin da yake yi masu jawabi a gidansa da ke Abuja, malamin shi'an ya zargi kasashen Amurka da Faransa da tunzara Najeriya ta aukawa Nijar.

Nijar
Bola Tinubu da tsohon shugaban Nijar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Duk da bambancin iyaka, mutanen Nijar da Najeriya, ‘yanuwan juna ne a cewar malamin.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Yi Kamari, Tinubu Ya Zauna da Gwamnonin da ke Iyaka da Jamhuriyyar Nijar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Aikin Faransa da Amurka ne?

"Kwatsam, Faransa da Amurka su na so su yi amfani da Najeriya domin yakar Nijar. Wannan abin ban mamaki ne domin Nijar da Najeriya daya ne.
Ko da mutanen kudancin Najeriya ba su ganin haka, mu a arewacin Najeriya, mu na da daulolin da Shehu Usman Danfodio da Kanem Borno su ka kafa.
Daga cikin kasashen daulolin nan ne aka yanki Najeriya da Nijar."

- Ibraheem El-Zakzaky

Kusancin kasashen Nijar da Najeriya

Jaridar ta ce Zakzaky ya dauko karatun tarihi, ya nuna Gazargamu ne babban birnin Kanem Borno, yanzu haka ya na tsakanin Najeriya da Nijar.

Shugaban na IMN ya ce an barkawa kasar Bornon yau ne da Najeriya, Kamaru, Chad da Nijar.

A rahoton Daily Trust, Zakzaky ya yi iirarin cewa mafi yawan garuruwan da su ke cikin kasar Borno a lokacin Shehu Danfodio, sun bar Najeriya.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Sultan, Fastoci Sun Bayyana Matsayarsu Kan Tura Soji Nijar Da ECOWAS Ke Shirin Yi, Sun Gargadi Tinubu

Idan aka duba taswira, ya ce za a samu wani yankin Gumel da Kazaure a cikin Nijar, haka abin yake a Katsina, har aka samu Katsinan Maradi a Nijar.

Iyakarta dai, garin Shehu Usman Danfodio na Marata ya na cikin Jamhuriyyar Nijar a yau, Zakzaky ya ce ba su goyon bayan a yaki wadannan mutane.

Sanatocin Arewa sun ja-kunne

Ana da labari cewa Sanata Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila ya na tsoron mummunan tasirin aukawa makwabtan Najeriya ta iyakar Arewa.

Sanatocin Arewa sun ankarar da gwamnati cewa idan yaki ya barke, zai shafi mutanen Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng