Faransa Ta Fara Kwashe Mutanenta Daga Nijar Bayan Soji Sun Hambarar Da Bazoum

Faransa Ta Fara Kwashe Mutanenta Daga Nijar Bayan Soji Sun Hambarar Da Bazoum

  • An fara kwashe yan asalin kasar Faransa da kasashen Turai daga Jamhuriyar Nijar
  • Ma'aikatar Turai da Harkokin Kasashen Waje ne ta bada sanarwar a ranar Talata, 1 ga watan Agusta bayan harin da aka kai ofishin jakadancin Faransa
  • Ana zaman zullumi a Jamhuriyar Nijar bayan sojoji sun yi juyin mulki sun hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niamey, Jamhuriyar Nijar - Faransa ta sanar da fara kwashe yan kasarta da sauran yan kasashen Turai daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki da sojoji suka yi a kasar a baya-bayan nan.

Ma'aikatar Turai da Harkokin Kasar Waje ta bayyana hakan cikin wata sanar, ta kara da cewa za a fara kwashe mutanen a yau, Talata, 1 ga watan Agusta, Premium Times ta rahoto.

Faransa za ta kwashe yan kasarta daga Nijar
Faransa Ta Fara Kwashe Mutanenta Daga Nijar Bayan Sojoji Sun Yi Juyin Mulki. Hoto: Emmanuel Macron
Asali: Facebook

Wani sashi na sanarwar ya ce:

Kara karanta wannan

Muddin Aka Yi Amfani da Sojoji a Nijar, A Shiryawa Yaƙi - Sojojin B/Faso da Mali

"Duba da halin da Niamey ke ciki, tashin hankalin da ya faru a ofishin jakadancinmu shekaran jiya da rufe iyakokin sama wanda ya hana yan kasarmu daman barin kasar don kashin kansu. Faransa na shirin kwashe yan kasarta da Turai ke niyyar barin kasar."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hankula sun kara tashi a Jamhuriyar Nijar yayin da Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaba

A bangare guda, Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Janar Abdourahmane Tchini, a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki mai ban mamaki.

Mutumin da aka yi wa lakabi da Omar Tchiani, ya yi juyin mulkin ne a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, lokacin da dakarun fadar shugaban kasa da ya ke jagoranci suka tsare shugaban kasar, Mohamed Bazoum.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Fadi Manyan Dalilai 13 Da Bai Kamata ‘Yan Najeriya Su Goyi Bayan Mamayar Jamhuriyar Nijar Ba

ECOWAS na duba yiwuwar amfani da karfin soji don mayar da Nijar hannun Bazoum

Hakazalika, Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, ECOWAS, ta ce akwai yiwuwar ta yi amfani da karfin soji domin mayar da Jamhuriyar Nijar kan turbar dimokradiyya bayan juyin mulkin hambarar da Mohamed Bazoum.

ECOWAS ta ba wa sabon shugaban sojojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani kwana bakwai ya mayar da Bazoum a matsayin shugaban kasa.

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sunyi Fatali Da Bukatar ECOWAS Na Mayar Ba Bazoum Kan Mulki

ECOWAS ta kuma umarci sojojin da su gaggauta sakin Shugaba Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan muƙamin shugabancin Jamhuriyar Nijar, Thisday ta rahoto.

Amma, a wani martani gaggawa, sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin sun yi watsi da kiran na ECOWAS tare da jan kunnen ƙungiyar da kada ta yi tunanin yin amfani da ƙarfin soji, rahoton The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dole Bazoum Ya Koma Mulki, Gwamnatin Amurka Ta Goyi Bayan Tinubu da ECOWAS

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164