Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS
- An dade ana yunkurin kafa kungiyar da za ta hada kan kasashen da ke karkashin yammacin Afrika
- A lokacin da Janar Yakubu Gowon da Gnassingbe Eyadema su na mulki a 1972 maganar tayi karfi
- Daga wancan lokaci zuwa yanzu, kungiyar ta ECOWAS ta yi karfi, ta samu shugabanni fiye da 30
Abuja – Rahoton nan ya nutsa tarihi, ya dauko jerin shugabannin Najeriya da su ka samu damar rike shugabancin kungiyar kasashen yammacin Afrika.
Bayanan da aka samu a shafin ECOWAS ya nuna wanda ya fara kokarin dunkule kasashen yammacin nahiyar Afrika shi ne Shugaba William Tubman.
Da yake mulkin Tanzaniya, Tubman ya jawo Cote d’Ivore, Guinea, Liberia da Sierra Leone.
An birne cibiyar ECOWAS a Legas
Bayan wani taro da aka yi a 1975 a garin Legas ne aka haifi wannan kungiya da har gobe ake alfahari da ita a bangaren siyasa da tattalin arziki a yankin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yanzu sau tara kenan shugabancin kungiyar ya na fadawa hannun shugabannin kasar nan. Hakan na zuwa bayan an zabi Bola Tinubu a Guinea Bissau.
Buhari ya yi sa'a, IBB ya dade
Janar Muhammadu Buhari ya jagoranci wannan kungiya har sau biyu, da farko a lokacin mulkin soja, sannan ya sake rike kujerar daga 2018 zuwa 2019.
Ibrahim Badamasi Babangida ne ya shafe shekaru kimani hudu ya na jan ragamar ECOWAS. A mata kuwa, Madam Ellen Johnson Sirleaf ta hau kujerar.
A baya-bayan nan, Olusegun Obasanjo ya na cikin wadanda su ka gama mulki ba tare sun jagoranci kungiyar ba, ko da ya rike wannan matsayi a mulkin soji.
Shehu Shagari wanda ya mulki Najeriya daga 1979 zuwa 1983 bai taba zama shugaban ECOWAS ba, haka Ernest Shonekan wanda bai dade a ofis ba.
A cikin shugabanni 34 da kungiyar ta samu, takwas daga Najeriya su ke. Hudu daga cikinsu sun zo a mulkin soja, ragowar a zamanin mulkin farar hula.
'Yan Najeriya a ECOWAS
1. Olusegun Obasanjo - 1978–1979
2. Muhammadu Buhari - 1985 –1985
3. Ibrahim Babangida - 1985 – 1989
4. Sani Abacha 1996 –1998
5. Abdulsalami Abubakar - 1998 – 1999
6. Umaru Musa Yar’Adua - 2008 –2010
7. Goodluck Jonathan - 2010 –2012
8. Muhammadu Buhari - 2018 – 2019
9. Bola Ahmed Tinubu - 2023 - Yau
Zuwan Tinubu Bissau
A karshen makon jiya mu kawo labari cewa Mai girma Bola Tinubu zai ziyarci kasar Afrika ta farko bayan zama Shugaban Najeriya a karshen watan Mayu.
‘Yan rakiya zuwa Bissau sun hada da masu ba shugaban kasa shawara da manyan jami’an Gwamnati, ana sa ran Mai girma Bola Tinubu zai dawo Najeriya.
Asali: Legit.ng