Akwai Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Sake Tashi a Najeriya a Dalilin Yunkurin OPEC

Akwai Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Sake Tashi a Najeriya a Dalilin Yunkurin OPEC

  • Wasu kasashen OPEC su na kokarin daga farashin gangar danyen mai domin samun karin riba
  • Najeriya ta na cikin kasashen da su ka fi kowa arzikin mai, amma ba ta da matatun da ke aiki
  • Farashin ya na hawa-da-sauka a kasar nan domin sai gwamnati ta shigo da man fetur daga ketare

AbujaThis Day ta ce babu mamaki farashin da mutanen Najeriya su ke sayen man fetur ya karu a sakamakon shirin da kungiyar OPEC take yi.

OPEC ta kasashe masu arzikin mai a Duniya na neman cigba da rage adadin danyen man da ake hakowa duk rana domin farashin ganga ya tashi.

Idan aka cigaba da tafiya a haka har zuwa watan Agusta, ana sa ran danyen mai ya kara tsada a kasuwa, hakan zai jawo canjin farashi a ko ina.

Kara karanta wannan

Diyar Biloniya, Hauwa Indimi, Ta Koka Bayan Ta Siya Tumatir Din N8,000, Jama'a Sun Yi Martani

Fetur
Aikin tace fetur Hoto: Getty Images/Jeremy Poland
Asali: Getty Images

80% na farashin fetur ya danganta ne da kudin gangar danyen mai a kasuwar Duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsadar danyen mai shi ne tsadar fetur

Rahoton ya ce zuwa yammacin jiya, an saida gangar danyen man Najeriya ne a kan $76.72, amma farashin gangar WTI na Amurka bai wuce $71.88 ba.

A kasuwar canji, mun lura duk ganga ta na tashi ne a kusan N60 000 a kudin Najeriya, sai maganar kudin tacewa da jigilar shi daga kasar waje.

Saudi ta zugo kasashen OPEC

Saudi Arabiya ta raina abin da ake samu daga mai, saboda haka ne ta rage adadin gangunan da ta ke hakowa da nufin farashin ya yi sama a kasuwa.

Kasar tayi nasarar zuga Rasha da Aljeriya da ke cikin OPEC wajen rage adadin man su. Kasashen uku sun ragewa Duniya ganguna miliyan 1.52 a kullum.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Na Hango N12bn Daga Sabon Harajin Motar da Tinubu Ya Kirkiro

IMF ta ce sai an saida gangar man Saudiyya a $80.90 kafin gwamnatin kasar Larabawan ta samu kudin da ta ke shirin kashewa a kasafin bana.

Najeriya ba ta raina kadan

Amma NNPCL na Najeriya ya gamsu da farashin gangar man. Shugaban kamfanin, Mele Kolo Kyari ya ce ko a $50 ake saida ganga, ba za su koka ba.

Gwamnatin tarayya ta na tsoron ta kora abokan cinikinta wajen neman riba. Idan OPEC ta samu yadda ta ke so, dole fetur zai zarce N540 a gidajen mai.

Ana samun saukin farashi

A wani rahoto da mu ka kawo, an fahimci cewa ana rage farashin fetur idan aka kamanta da yadda da ‘yan kasuwa su ka saida man a makon jiya.

A tashohin ‘yan kasuwa ana saida lita tsakanin N495 zuwa N496, bayan ya haura N503 a baya, a tashoshin kamfanin NNPC ne farashi bai canza ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng