Yan Najeriya Sun Yi Bajinta, Yayin Da Suka Zo Na 2 A Ma'aikata Mafi Kwazo A Duniya
- Ma'aikatan Najeriya sun ciri tuta, a yayin da aka ayyanasu na biyu a jerin ma'aikata mafi ƙwazo a duniya
- Wani rahoto na ƙididdiga da aka gudanar ne ya bayyana hakan a cikin wata sabuwar wallafa da aka yi
- Rahoton ya ce ma'aikatan Najeriya kan shafe sa'o'i aƙalla 2,124 suna aiki ba tare da gajiyawa ba a duk shekara
Ma’aikatan Najeriya sun zo na biyu a duniya bayan na ƙasar Mexico a jerin ma’aikatan da suka fi aiki tukuru a duniya, ta hanyar shafe sa’o’i 2,124 da kowane ma’aikaci ke yi a duk shekara.
A wani rahoto da jaridar Vanguard ta fitar a ranar Alhamis, Najeriya ce ƙasar da ke da mafi kwazon ma'aikata a nahiyar Afrika.
Kasar da ta fi Najeriya ma'aikata masu ƙwazo, da waɗanda ke bin Najeriya
Ma’aikatan ƙasar Mexico da suka zo na ɗaya, sun fi na Najeriya da sa’o’i huɗu ne kacal a duk shekara inda suke yin sa'o'i 2,128 suna aiki, a cewar rahoton.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A Najeriya, lokutan aiki na mafi yawan ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu ba ya wuce sa'o'i takwas, wanda zai iya kasancewa daga 8 zuwa 4 ko kuma 9 zuwa 5 daga Litinin zuwa Juma'a, kamar yadda New Telegraph ta wallafa.
Saidai wasu ma'aikatun kamar gidajen watsa labarai, asibitoci, hukumomin tsaro da masana'antu, sukan buƙaci ƙarin kwanaki da sa'o'i na ma'aikatansu, inda sukan gudanar da aiki a ranakun Asabar da Lahadi a tsarin karɓa-karɓa.
A yanayi na yau da kullum, ma'aikata kamar mata da ke saide saide a kasuwanni da sauran masu shaguna, sukan yi aiki har zuwa sa'o'i goma ko fiye da haka a kowace rana.
Duk da cewa rahoton bai yi bayani kan nau'in ayyukan da aka yi amfani da su ba, ya nuna cewa ƙasashen da ke kan gaba ba su da ci gaban fasaha sosai.
Ƙasashen da ke biye da Najeriya a wajen ƙwazon ma'aikata
Sauran ƙasashen da suke biye da Najeriya sune; Costa Rica wacce ta zo na uku da sa’o’i 2,073, sai Colombia ta huɗu da sa'o'i 1,964, sannan sai Chile ta biyar da sa'o'i 1,916.
Abin mamaki kuma shi ne, duk da kasancewar Koriya ta Kudu ƙasar da take amfani da fasahohin zamani, ta shigo cikin jerin a matsayin ta shida inda ma'aikatan ƙasar ke shafe sa'o'i 1,910 suna aiki a shekara.
Ma'aikatan ƙasar Amurka, wacce akewa kallon mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya, sukan yi aiki na tsawon sa'o'i 1,791 a shekara, wanda hakan ya ajiyesu a matsayi na 13.
Ma'aikatan ƙasar Japan, wacce ita ce ta uku mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya, sun kasance sune na 30 a jerin ma'aikata masu ƙwazo a duniya, inda suke shafe sa'o'i 1,607 suna aiki a kowace shekara.
Tinubu ya kafa kwamiti kan batun ƙarin albashin ma'aikata
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan cewa, shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamiti na musamman kan ƙarin albashin ma'aikatan ƙasar.
Hakan dai ya biyo bayan cire tallafin man fetur da shugaban ya yi a ranar da ya karɓi rantsuwar fara aiki.
Asali: Legit.ng