Elon Musk: Ban Samu Tallafin Komai Ba Daga Mahaifina Ba Bayan Na Gama Makaranta

Elon Musk: Ban Samu Tallafin Komai Ba Daga Mahaifina Ba Bayan Na Gama Makaranta

  • Attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya Elon Musk ya ce mahafinsa bai samu halin tallafa masa da kuɗaɗe ba a yayin da yake tasowa
  • Ya ce hakan ya jefa rayuwarsa da ta ɗan uwansa cikin hali na ƙunci saboda su suka cigaba da taimakon mahaifin nasu
  • Musk ya ce mahaifinsa bai bar masa komai na gado ba, kuma bai taɓa samun wata kyauta babba ta kuɗi ba

Amurka - Fitaccen attajirin nan da ya fi kowa kuɗi a duniya wato Elon Musk wanda shine ke da kamfanin Tesla da kuma Tuwita, ya bayyana cewa mahaifinsa bai samar masa da wani tallafi na kuɗi ba bayan kammala karatunsa.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita yayin da ya ke maida martani ga wani rubutu da wani ya yi, inda ya ke bayyana cewa Elon ya fito daga gidan masu wadata amma kuma ya zo ya yi ta fama da rayuwa ta ƙunci da matsin tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari

Elon Musk
Mai Kudin Duniya Elon Musk. Hoto: Elonmusk
Asali: Getty Images

Ban samu rayuwar jin dadi ba a lokacin kuruciya ta

Elon Musk ya ƙara da cewar bai samu rayuwa ta jin daɗi ba a lokacin da ya ke tasowa saboda ƙarancin tallafi da ya samu daga iyayensa saboda hali na rashin abin hannu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Musk ya kuma bayyana irin gwagwarmayar da mahaifinsa ya sha wajen ƙoƙarin kula da shi da kuma 'yan uwan shi inda ya bayyana cewa mahaifin nasu ya kasance ya na da wani kamfani da ya kai aƙalla shekaru 20 ya na aiki kafin abubuwa su sauya daga baya.

Mahaifina ne ya samu karayar arziƙi

Kamar yadda The Cable ta samu, Elon Musk ya bayyana cewa mahaifinsa wato Errol Musk ya samu karayar azriƙi ta tsawon shekaru 25 wanda a wannan lokacin ne shi da dan uwansa suka shiga cikin halin ƙunci na rayuwa.

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Labarin Wani Matashin Da Ya Dirkawa 'Yan Mata 3 'Yan Gida Daya Ciki

A kalaman Elon Musk:

“Na taso ne daga gidan marasa ƙarfi zuwa na masu matsakaicin ƙarfi, amma duk da haka ban samu wani jin daɗin rayuwa ba da ina yaro, kuma ba a bar min gadon komai ba, sannan babu wani da ya taɓa bani wata kyauta babba ta kuɗi.”
“Babana ya buɗe wani kamfani na Injiniyanci da kanikanci wanda ya yi sharafinsa na tsawon shekaru 20 zuwa 30, amma daga bisani ya karye, ta yadda sai ni da kuma ɗan uwa na mu ka ci gaba da taimakonsa.”

Duk da rashin samun tallafi na kuɗaɗe daga wurin mahaifinsa, Elon Musk ya yaba masa bisa koya masa ilimummuka da suka shafi fasaha, ilimin ƙere-ƙere da kuma ilmin gina abubuwa.

An samu mai kudin da ya hau saman Elon Musk

A cikin watan Afrilun shekarar 2023 da ya gabata ne dai aka samu wani attajiri dan kasar Faransa mai suna Bernard Arnault da ya hau saman Elon Musk a jerin masu kudin duniya.

Hakan dai ya biyo bayan karuwar ribar da Bernard Arnault din ya samu a kamfanonin shi Louis Vuitton, Christian Dior, Givenchy, Tiffany’s, Marc Jacobs, da Sephora a farko-farkon shekarar nan da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel