An Karrama Jonathan a Kasar Waje Kan Abin da Ya Yi a Najeriya Shekaru 8 da Suka Wuce

An Karrama Jonathan a Kasar Waje Kan Abin da Ya Yi a Najeriya Shekaru 8 da Suka Wuce

  • Heritage Times (HT) ta karrama Goodluck Jonathan da lambar yabo a babban birnin kasar Ruwanda
  • Marigayi John Magufuli, Seretse Ian Khama sun samu kyauta tare da Tsohon shugaban na Najeriya
  • Dr. Jonathan wanda ya yi mulki tsakanin 2010 da 2015 ya yi kira ga shugabannin Afrika a wajen taron

Kigali - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga shugabannin Afrika da su yi kokarin inganta rayuwar talakawan da suke mulka.

Premium Times ta rahoto Dr. Goodluck Jonathan yana cewa yin hakan ne kurum zai sa a cigaba da tuna shugabannin ko bayan sun bar karagar mulki.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan kira yayin da ya karbi lambar yabo a matsayin Gwarzon Damukaradiyya kuma Jakadan zaman lafiya a Afrika.

An ba Jonathan wannan kyauta ne a karshen makon jiya a birnin Kigali da ke kasar Ruwanda. Wannan ne karon farko da aka shirya irin taron a tarihi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Kiran da Goodluck Jonathan ya yi

A jawabin da ya gabatar, Vanguard ta ce Jonathan ya yi kira ga shugabannin kasashen nahiyar su maida hankali a kan hakkoki da walwalar al’ummarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda yake fada a taron, nauyi ne a kan jagorori da su tafiyar da kasarsu da kyau, su kuma guji kawo tsare-tsaren da za su wahalar da Bayin Allah.

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan wajen jana'iza a coci Hoto: @GEJonathan
Asali: Twitter

A wajen taron, an bada lambar girma ga tsohon shugaban kasar Tanzaniya, Marigayi John Magufuli.

Wadanda da suka shirya bikin sun bada kyauta ga tsohon mataimakin shugaban Liberiya, Jewel Howard-Taylor da tsohon shugaban Botswana, Seretse Khama.

A karshe, Jonathan ya godewa Heritage Times da suka shirya irin wannan taro domin a karfafa gwiwar shugaban kasashen Afrika wajen taimakon jama’a.

Shekaru biyar kurum nayi ina mulkin Najeriya. Nayi imani cewa ‘yan gudumuwar da na bada a wannan lokaci da bayan ofis ne suka gamsar da masu shirya taron nan, suka karrama ni a matsayin gwarzon Damukaradiyya da zaman lafiya a Afrika.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

Hakan ya na nufin ba dadewan shugaba a kan mulki ne mafi muhimmanci ba, a’a, abin da mutane za su tuna shi ne yadda ka yi mulki da tasirinka a ofis.

- Goodluck Jonathan

Aiki a gaban Tinubu

Idan aka yi sake, an ji labari kungiyoyin kwadago da na ‘yan kasuwa za su fito su yi wa Gwamnatin Bola Tinubu zanga-zanga da zarar ya shiga ofis a Mayu.

Hakeem Ambali ya tabbatar da cewa kungiyar NLC ba ta goyon bayan a janye tallafin man fetur a kasar nan, wannan shi ne ra'yin kungiyar TUC da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng