Bayan Shafe Shekaru 34 A Gidan Yari, Mutumin Da Aka Yi Wa Daurin Shekaru 400 Bisa Kuskure Ya Samu Yanci

Bayan Shafe Shekaru 34 A Gidan Yari, Mutumin Da Aka Yi Wa Daurin Shekaru 400 Bisa Kuskure Ya Samu Yanci

  • Sidney Holmes, wani mutum dan shekara 57 da aka yanke wa hukuncin shekara 400 a gidan yari ya samu yanci
  • Hakan na zuwa ne bayan Holmes ya shafe fiye da shekara 34 a gidan yarin, amma ya sake neman a waiwayi shari'arsa yana mai cewa yana da gaskiya
  • Bincike da ofishin Antoni Janar na Broward ta yi ya nuna akwai kuskure wurin alakanta Holmes da fashin da kuskure, alkalai biyar cikin shida sun amince a sake shi

Amurka - Wani mutum wanda ya shafe fiye da shekaru 30 cikin 400 da aka yanke masa ya shaki yancin iska a ranar Litinin, 13 ga watan Maris.

An tura Sidney Holmes, dan shekara 57, gidan yari ne a Afrilun 1989 kan wani fashi da aka yi zargin ya yi a 1988 da aka ce shine direban yan fashin.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Aika Muhimmin Sako Ga Masu Neman Aikin da Hukumar Za Ta Dauka

Sidney Holmes
Sidney Holmes bayan an wanke shi a kotu a ranar Litinin. Hoto: Carline Jean/South Florida Sun-Sentinel/Tribune News Service
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan uwan Holmes sun taho sun tarbe shi a yayin da aka sako shi a ranar Litinin, kuma abu na farko da ya ce shine yana son ya nemi wani abu ya ci, CBS Miami ta rahoto.

Antoni Janar na Broward State Harold F ya ce:

"Doka daya gare mu a nan a ofishin Antoni Janar na Broward - a yi abin da ya dace a kowanne lokaci. A matsayin masu bincike, ajandar mu kawai ita ce inganta tsaro a garuruwanmu da tabbatar da adalci.
"Na jinjinawa wanda abin ya faru da su, shaidu, jami'an tsaro saboda taimakon da suka yi wurin sake bincikar laifin da ya faru fiye da shekaru 34 da suka shude."

Yadda Holmes ya samu yancinsa

Holmes ya tuntubi ofishin bibiya na Antoni Janar (CRU) a 2020 ya fada wa masu binciken bai aikata laifin ba. CRU din sun duba suka ce akwai yiwuwar Holmes na da gaskiya.

Kara karanta wannan

Asiri Zai Tonu, Shugabannin Jam’iyyar APC Na Fada Kan Zargin Cinye Kudin Kamfe

Yayin bincike shari'ar Holmes, an gano cewa shaidan da ganau ya bada akwai kuskure kuma babu hujja da ke hada Holmes da fashin.

Pryor ya ce, binciken da daya cikin yan uwan wanda abin ya faru da shi ya gano cewa akwai yiwuwar an yi kuskuren alakanta motar Holmes da fashin kuma ba a yi la'akari da banbancin da ke tsakanin motarsa da wacce yan fashin suka yi amfani da shi ba.

Bisa binciken, biyar cikin shida na masu binciken sun cewa Holmes yana da gaskiya kuma a yi watsi da hukuncin da aka masa nan take.

Wadanda aka yi wa fashin suma sun ce suna ganin a saki Holmes. Yan sanda da suka yi ainihin binciken suma sun yi mamakin cewa Holmes ya yi shekaru 34 cikin 400 da aka yanke masa.

Wata kungiyar tallafawa al'umma OIC ta South Florida za ta taimakawa Holmes ya koma cikin al'umma, tare da ba shi horaswar samun aikin.

Kara karanta wannan

An Kama Bokan Da Ke Yi Wa Mutane Alkawarin 'Azirta' Su Ba Tare Da Amfani Da Sassan Jikin Dan Adam Ba A Edo

An tura surukin Obasanjo gidan yari, zai yi shekaru 7

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu ta musamman ta yanke wa Dr John Abebe, surukin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan gyaran hali saboda almundahana.

Alkalin kotun, Mai shari'a Mojisola Dada amma ta bada zabin biyan tara na naira miliyan 50.

Asali: Legit.ng

Online view pixel