"Mu Yi Aiki Tare", Shugaban Ukraine, Zelenskyy Ya Tura Sakon Taya Murna Ga Bola Tinubu

"Mu Yi Aiki Tare", Shugaban Ukraine, Zelenskyy Ya Tura Sakon Taya Murna Ga Bola Tinubu

  • Shugabannin kasashen duniya na cigaba da taya zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, murnar cin zabe
  • Volodymyr Zelenskyy, shugaban kasar Ukraine ya shiga jerin shugabanin kasashen duniya da suka taya Tinubu murnar lashe zaben
  • Zelenskyy ya ce yana fatan yin aiki tare da gwamnatin Tinubu wurin magance matsalolin da ke adabar duniya kamar rashin abinci

Shugaban kasar Ukraine da ke fama da yaki, Volodymyr Zelenskyy, ya taya Bola Ahmed Tinubu, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, APC, murna bisa nasarar da ya samu a zaben da aka kammala a baya-bayan nan.

Zelenskyy, a shafinsa na Twitter, ya nuna cewa a shirye ya ke ya yi aiki tare da Tinubu don magance kallubalen da duniya ke fama da su ciki har da barazanar karancin abinci.

Zelenskyy da Tinubu
Shugaban Ukraine, Zelenskyy da Bola Tinubu. Hoto: Sahara Reporters.
Asali: Twitter

Kungiyoyi da daidaikun mutane daban-daban sun yi korafi kan zargin magudi da rashin bin ka'idojin zabe da hukumar INEC ba ta yi ba, suna nema a hukumar Mahmood Yakubu, shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Ku Da Kanku Kun Amince Akwai Kura-Kurai A Zaben, Atiku Ya Fada Wa Bangaren Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da takwararsa na jam'iyyar Labour, Peter Obi sun ki amincewa da sakamakon zaben, sun kuma ce za su tafi kotu.

Ina fatan za mu yi aiki don magance kallubalen duniya, Zelenskyy ga Tinubu

Shugaban na Ukraine a shafinsa na Twitter ya ce:

"Ina taya ka murna @OfficialABAT kan lashe zaben shugaban kasar Najeriya. Ina fatan hadin kai. Ina da yakinin hakan zai karfafa hulda tsakanin kasashen biyu. Ukraine ta shirya don aiki tare don shawo kan kallubalen duniya, ciki har da barazanar samar da abinci."

A ranar Juma'a, Sahara Reporters ta rahoto cewa zaben jin ra'ayin mutane ya nuna cewa dukkan manyan jam'iyyu hudu da suka tsayar da yan takarar shugaban kasa sun yi magudin zabe, siyan kuri'u da wasu laifukan zaben.

Kara karanta wannan

Toh fa: Kotu ya kada hantar Tinubu, ya saurari bukatar Atiku da Obi 1 kan zaben 25 ga wata

Jam'iyyun da aka samu da laifin sun hada da jam'iyyar All Progressive Congress (APC), People Democratic Party, (PDP) Labour Party, (LP) da New Nigeria Peoples Party, (NNPP).

Sarki Mohammed VI na Morocco ya taya Bola Tinubu murnar cin zabe

Tunda farko, kun ji cewa Sarki Mohammed VI na kasar Morocco ya mika sakon taya murna ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasar Najeriya.

Sarki Mohammed ya ce yana fatan karfafa alakar zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya a karkashin gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel