Saudi Arabiya ta Cafke ‘Yan Najeriya 800, An Yi Bayanin Laifuffukan da Suka Aikata
- Jami’an kasar Saudi sun yi ram da wasu mutane da ‘Yan Najeriya ne da aka samu da aikata laifuffuka
- Zargin da Gwamnatin Saudi take yi shi ne akwai mutane 40, 000 da suka shigo mata ba tare da ka’ida ba
- Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga masu zuwa Saudi Arabiya su tanadi duka takardun da ake bukata
Saudi Arabia - Gwamnatin Saudi Arabiya ta cafke wasu mutane da ake zargin ‘Yan Najeriya ne, kuma an tsare su a dalilin aikata laifuffuka.
Punch da ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, ta ce kimanin mutanen Najeriya 800 ake zargi da aikata laifuffukan da suka shafi harkar gudun hijira.
Bayanin cafke wadannan Bayin Allah yana cikin wani jawabi da ya fito daga bakin hukumar da ke kula da sha’anin masu ci-rani a kasar waje.
Gabriel Odu wanda shi ne babban jami’in hulda da jama’a a hukumar ya fitar da jawabi a dazu.
Ayi hattara da zuwa Saudi - Gabriel Odu
A jawabin Gabriel Odu, an fahimci hukumomin Saudi Arabiya sun tabbatar da akwai mutane 45, 458 da suka shigo cikin kasar ba tare da bin ka’ida ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Cable ta tabbatar da tun a watan Oktoban 2022 aka fara kama wadanda suke zaune a kasar Saudi Arabiya ba tare da samun izinin gwamnati ba.
A dalilin abin da ya faru, gwamnatin tarayya tayi kira ga ‘Yan Najeriya da ke shirin yin balaguro zuwa kasar Larabawan, su tanadi duka takardunsu.
Gwamnatin Najeriya ta ankarar da jama’a cewa jami’an Saudi sun kara kaimi wajen yin ram da duk wadanda suke zama ba tare da izinin hukuma ba.
Jawabin hukumar kula da ci-rani
“Hankalin hukumar kula da sha’anin ‘Yan Najeriya da ke ci-rani ya je ga wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnati.
Jami’an harkokin Saudi Arabiya sun zafafa a kan masu zama a kasarsu ba tare da takardu ba.
Wasikar ta ce daga Oktoba zuwa Disamban 2022, jami’an hadin gwiwar Saudi sun maida hankali wajen kama ‘Yan gudun hijira da suka saci hanya.
Dubban mutanen da suka shiga Saudi sun aikata laifuffukan da suka shafi tsallaka iyaka ba tare da izini ba, sabawa dokar aiki da cin zarafin yara.
Za ayi zabe a Najeriya - Buhari
A wani rahoto da aka fitar, an ji Lai Mohammed ya ce babu shirin kawo Gwamnatin rikon kwarya, domin Bola Tinubu ne zai zama Shugaban kasa.
Hadimin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya karyata zargin Nasir El-Rufai da Abdullahi Ganduje na cewa ana kokarin a fasa shirya zaben bana.
Asali: Legit.ng