Kare ya Bindige Ubangidansa Bayan Ya Bar Bindiga a Mazaunin Bayan na Motarsa

Kare ya Bindige Ubangidansa Bayan Ya Bar Bindiga a Mazaunin Bayan na Motarsa

  • An tsinci gawar wani ba Amurke a motarsa, inda 'yan sanda suka tabbatar da yadda karensa ya shekesa bayan dira kan bindigarsa
  • Binciken da jami'an 'yan sanda su ka yi, ya bayyana yadda a ka yi harbin ta kujerar baya duba da nan ne saitin inda mutumin ke zaune
  • Lamarin mai ban tausayi ya yi sanadiyyar barin mafaraucin da mummunan rauni, gami da rasa rayuwarsa ta ke yanke

Wani mutumi ya mutu daga raunin harsashin harbin da karensa ya masa bisa kuskure yayin da ya ke tsalle-tsalle a cikin motarsa.

Kalbu
Kare ya Bindige Ubangidansa Bayan Ya Bar Bindiga a Mazaunin Bayan na Motarsa. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

Mutumin wanda 'dan Kansas ne na birnin US, ya rasa ransa ta hanyar harbi bisa kuskure yayin da ya ke kan hanyarsa ta farauta wanda karensa ya masa.

An tabbatar da yadda mutumin ya ke zaune a kujerar direba yayin da karen ke zaune a kujerar baya cikin motar a lokacin da lamarin ya auku.

Kara karanta wannan

Allah ya sa: Buhari ya yiwa 'yan Najeriya alkawari mai zafi, zai cika kafin ya sauka mulki

Rahotannin 'yan sanda sun bayyana yadda suke kan hanyarsu na farauta amma mutumin ya ajiye bindigarsa a kujerar baya inda karen ke zaune.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda rahotannin 'yan sandan suka bayyana, mutumin mai shekaru 32 ya rasa ransa ranar Asabar, 21 ga watan Janairu.

Haka zalika, rahoton ya tabbatar da yadda karen mafaraucin yayin da ya ke kujerar baya ya dira kan bindigar, wanda hakan ya janyo bindigar ta saici gefen mai karen.

Jaridar Mirror ta ruwaito yadda mafaraucin ya samu matsanantancin rauni, wanda ya yi sanadiyyar rayuwarsa ta yanke.

Kamar yadda jami'an 'yan sanda suka bayyana:

"Wani karen farauta mallakin wani mutumi a wata mota dauke da bindiga ya dira kan bindiga wanda haka ya janyo ya bindige mai shi."

Tun daga Amurka Budurwa ta hau jirgi zuwa Afrika don neman man kadanya

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Wa Samanja Kisar Gilla A Cikin Gonarsa A Neja

A wani labari na daban, wata budurwa ta shayar da jama'a mamaki bayan ta hau jirgin sama tun daga Amurka har Afrika don neman man kadanya.

Kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo da ya yadu a TikTok, ta sanar da cewa ingantaccen man kadanya yana Afrika.

Hakan yasa tayi dirar mikiya tare da siyansa mai tarin yawa sannan ta hau jirgi tare da komawa Amurka, lamarin da ya ba jama'a mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel