IGP ya Samu Takardar Umarnin Damko ‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Akwa Ibom

IGP ya Samu Takardar Umarnin Damko ‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Akwa Ibom

  • Wata babbar kotun majistare ta umarci sifeta-janar na 'yan sanda da ya cafko 'dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom karkashin jam'iyyar PDP
  • Hakan ya biyo bayan an zargesa da yaudara da ha'inci, amma ya ki halartar zaman kotu, wanda hakan yasa aka bada umarnin kama shi a ranar 23 Disamba 2023
  • Sifeta-janar din ya amince da kawo Emo ne bayan takardar umarnin ta riskesa ranar 9 ga watan Junairu ta hannun kwamishinansa

An umarci sifeta-janar na 'yan da ya damko Umo Eno, 'dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom. A halin yanzu ana sa ran ya gaggauta aiwatar da hakan.

Eno Akwa Ibom
IGP ya Samu Takardar Umarnin Damko ‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Akwa Ibom. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, wata babbar kotun majistare a Wuse zone 6 dake birnin tarayya (FCT), ta bada umarnin cafke Eno a ranar 23 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Edo: 'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Shugaban Alkalan Kotun Gargajiya ta Jihar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Emmanuel Iyanna, babban alkalin majistare ne ya bada umarnin kamun bayan kama 'dan takarar gwamnan da laifukan da suka shafi "yaudara da ha’inci a kayyaki."

Wata majiya ta tabbatarwa TheCable yadda Eno yaki halartar kotun, daga bisani aka saurari karar baya kotu, wanda hakan ce yasa aka bukaci kama shi.

Kara mai lamba CR/96/2022 ita ce wacce Edet Godwin Etim ya shigar.

Kungiyar kamfen din Eno ya musanta masaniya game da karar da aka shigar.

A umarnin kamun, babban alkalin majistaren ya ce:

"An umarce ka da ka damko wannan faston Umo Bassey Eno gami da gurfanar da shi gaba na.

An ba IGP umarnin kamun ne ta kwamishinan 'yan sanda.

Kwafin amincewar da jaridar The Cable ta gani ya nuna yadda aka buga tambari "an karba" ranar Litinin, 9 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar, FG

Eno, wanda gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel ke marawa baya, ya zama zakaran gwajin dafin jam'iyyar a zaben fidda gwanin da ya gabata a watan Mayun 2022.

Ya sumu kuri'u 993, yayin da wakilan zabe 1,018 suka kada kuri'u a zaben.

Ya dankara abokin hamayyarsa mafi kusa - Onofiok Luke, 'dan majalisar tarayya, wanda ya samu kuri'u biyu kacal; da kuma Bassey Albert, sanata, wanda ya samu kuri'a daya tol.

Alkali yayi umarnin cafko 'dan takarar gwamnan PDP na Akwa Ibom

A wani labari na daban, alkalin kotun majistare da ke babban birnin tarayya na Abuja ya umarci cafko masa 'dan takarar gwamnan PDP na jihar Akwa Ibom.

Eno shi ne na gaban goshin gwamna Emmanuel Udom na jihar wanda yayi nasarar yin caraf da tikitin jam'iyyar na kujerar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel