Gwamnatin Birtaniya Ta Gayyaci Malaman Najeriya Aiki, Za Ta Biya Albashi Mai Tsoka Na Miliyoyin Naira

Gwamnatin Birtaniya Ta Gayyaci Malaman Najeriya Aiki, Za Ta Biya Albashi Mai Tsoka Na Miliyoyin Naira

  • Gwamnatin kasar Birtaniya na yi wa malaman Najeriya tayin albashin Naira miliyan 15 duk shekara
  • Wata sanarwa da aka fitar a shafin gwamnatin na Birtaniya ta ce malaman da suka cika sharudan suna iya neman aikin
  • Kasashen da aka ce za su iya neman aikin sun hada da Najeriya, Ghana, Singapore, Afirka ta Kudu, Hong Kong da sauransu

Daga watan Fabrairun shekarar 2023, malaman Najeriya da suka yi hijira zuwa Birtaniya za su rika samun albashin N15.065 miliyan duk shekara.

Bayanai daga shafin intanet na gwamnatin Birtaniya ya bada sharuda da dokoki ga mutanen da ba yan Birtaniya ba amma ke da sha'awar koyarwa a kasar, ya ce albashi zai danganta da cancanta da kuma kasar da malamin ya fito.

Malamai a UK
Gwamnatin Burtaniya Ta Gayyaci Malaman Najeriya Aiki, Za Ta Biya Albashin Naira Miliyan 15 A Shekara. Hoto: SolStock
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

Jerin kasashen da aka amince su nemi aikin

A cewar rahoton, Birtaniya, a farkon watan Disamba ta ambaci Najeriya cikin jerin kasashen Afirka wadanda yan kasar za su iya neman biza na koyarwa ta hukumar kula da koyarwa a Birtaniya, daga Fabrairun 2023.

Sauran kasashen sun hada da Ghana, Hong Kong, Indiya, Jamaica, Singapore, Afirka ta Kudu, Ukraine da Zimbabwe.

The Punch ta rahoto cewa wadanda za su nemi aikin ba su bukatar kwarewa na koyarwa domin kasar za ta bada horaswa ga masu sha'awar yin hijira zuwa can.

Daga bayanai a kasar Birtaniya, dukkan malaman da suka cancanta za a rika biyansu a kalla fam 28,000 ko fiye da hakan idan suna aiki a Landan.

Makarantu za su iya yi wa malamai karin albashi

Kowane makaranta za ta zabi albashin da za tabiya malaman da suka cancanta. Za a rika karin albashi ne bisa kwazon aiki ba dadewa a aiki ba kuma duk shekara za a rika karin.

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi kudaden da ya kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a cikin shekaru 3

Sanarwar ta ce:

"Idan za ka iya nuna kwazo a harkokin koyarwa, za a iya sanya ka cikin malamai masu karbar albashi mafi tsoka. Wannan ga malamai ne da ke bada gudunmawa mai muhimmanci kuma mai dorewa ga makarantarsu."

Jihohin da ake biyan malaman makaranta mafi karancin albashi na N30,000 a Najeriya

Malaman makarantun firamare da sakandare a jihohi 15 da kuma birnin tarayya Abuja ne kawai suke karbar mafi karancin albashi na N30,000 duk wata.

Duk da cewa an shafe shekaru uku bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar a cewar kungiyar malaman Najeriya, NUT, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel