Elon Musk Ya Dawo da Asusun Twitter Na Trump, Shekaru Biyu Bayan Korarsa
- Kafar sada zumunta ta Twitter ta dage dakatarwar da ta yiwa tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump bayan jin ra'ayin jama'a
- An dakatar da Trump ne a 2021 bayan da rikici ya barke a Amurka bayan gudanar da zaben shugaban kasa
- Elon Musk na ci gaba da bayyana maganganu masu daukar hankali tun bayan da ya karbi ragamar Twitter
Twitter - Kamfanin Twitter ya maido da asusun tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump kan manhajar bayan dogon lokaci yana kasa.
Wannan na fitowa ne daga bakin sabon mai kamfanin, Elon Musk a wani rubuta da ya yada a kafar a ranar Juma'a, inda ya nemi ra'ayin jama'ar Twitter kan yiwuwar dawo da Trump.
Kuri'un da jama'a suka kada a kafar ya nuna cewa, akalla kaso 51.8% ne suka nuna sha'awar Trump ya dawo, yayin da kaso 48.2% suka nuna kin hakan. Akalla mutane miliyan 15 ne suka kada kuri'a.
Bayan haka ne Musk ya rubuta cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jama'a sun yi magana, Za a maido da asusun Trump."
Ya kuma bayyana cewa, muryar jama'a ita ce muryar ubangiji, don haka ya zabi abin da al'umma suka fada don dawo da tsohon shugaban kasar.
Yadda aka dakatar da asusun Trump
Idan baku manta ba, an dakatar da asusun Trump daga Twitter ne a Janairun 2021 bayan da rikici ya barke bayan zaben 2020 da aka gudanar a Amurka, TheCable ta ruwaito.
Ya zuwa yanzu dai Trump bai rubutu ko martani game da maido da asusunsa ba tun bayan da manhajar ta sahhale masa sake dandana zakinta.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Trump ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyarsu ta Republican a zaben 2024 mai zuwa.
A lokacin mulkinsa na baya, Trump na amfani da Twitter a matsayin kafar bayyana ra'ayoyinsa da yada maganganu masu jawo cece-kuce.
Ya zuwa yanzu dai Trump na fuskantar bincike daga gwamnatin Amurka kan wasu matsaloli da suka shafi shugabancin da ya yi na wa'adi daya a baya.
Hakazalika, a makon da ya gabata ne Donald Trump ya aurar da diyarsa ga wani dan Najeriya mazaunin kasar waje.
An yi daurin auren ne shekara guda bayan da aka yi baikonsu a wani biki mai kayatarwa, an yi ta cece-kuce a kai.
Asali: Legit.ng