Lalata da dalibai domin basu maki a jarrabawa: An kori babban lakcara a jami'ar Najeriya

Lalata da dalibai domin basu maki a jarrabawa: An kori babban lakcara a jami'ar Najeriya

Jami’ar Lagas ta dakatar da Boniface Igbeneghu, wani Lakcara na makarantar kan laifin neman lalata da wata yarinya da ta je a matsayin mai neman a dauke ta shiga jami’ar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban jami’ar Lagas, Oluwatoyin Ogundipe, yace an dakatar da lakcaran har sai baba ya gani a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba.

Yace: “An kafa wani kwamiti domin su binciki lamarin.”

An fallasa Boniface wanda ya kuma kasance fasto a Cocin Foursquare Gospel Church, a cikin wani bidiyo na minti 13 da BBC Africa Eye ta saki a ranar Litinin.

Wata ‘yar jarida da ta yi basaja, a matsayin daliba mai neman shiga makarantar c eta fallasa bidiyon.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya na gab da kwace kadarorin Maina na miliyoyin naira a Najeriya da kasar waje

An tattaro cewa lakcaran bai san cewa duk abin da ya yi mata na kokarin yin lalata da ita, tna daukar bidiyon sa ba.

A cikin bidiyon, lakcaran ya hadu da dalibar a ofishinsa inda yace ya san yadda zai samu duk wata yarinya da yake so.

Yace: “Baki san cewa ke kyakyawa bace? Kin san cewa ni fasto ne sannan ina a ganiyar shekaru 50 da doriya amma idan ina son yar shekara 17, kawai abunda nake bukata shine dadin baki da bayar da wasu yan kudade."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel