Diyar Tsohon Shugaban Kasan Amurka Zata Auri ‘Dan Najeriya, Shagulgula Sun Kankama

Diyar Tsohon Shugaban Kasan Amurka Zata Auri ‘Dan Najeriya, Shagulgula Sun Kankama

  • Diyar tsohon shugaban kasan Amurka, Shugaba Donald Trump, zata auri wani matashin Najeriya mai suna Michael Boulos wanda ya girma a Najeriya
  • Mahaifi da mahaifiyar Boulos ‘yan asalin kasashen Lebanon ne da Faransa da suka kafa kasuwancinsu a Legas kuma a nan suka yi rayuwa da ‘ya’yansu
  • Za a yi auren a ranar 12 ga watan Nuwamba a kasar Girka inda a halin yanzu ake ta shirya gagarumin shagalin babbar ranar dake zuwa

Amurka - Diyar tsohon shugaban kasan Amurka Donald Trump, ta hudu, Tiffany, ta shirya aure da masoyinta Michael Boulos a kasar Girka a wani katafaren gabar ruwa mai cike da bishiyoyin kwakwa wanda mallakin mahaifinta ne a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Tiffany da Boulos
Diyar Tsohon Shugaban Kasan Amurka Zata Auri ‘Dan Najeriya, Shagulgula Sun Kankama. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Boulos a jihar Legas ya girma kuma ‘dan Najeriya ne saboda a kasar aka haifesu. Mahaifinsa da mahaifiyarsa ‘yan asalin Lebanon ne da Faransa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yar Baiwa Daga Najeriya Mai Shekara 13 Ta Kafa Tarihin Shiga Jami’a a Kasar Amurka

‘Dan Najeriya ne Boulos saboda a nan ya girma

Ya dawo Najeriya a shekarun yarintarsa inda kasuwancin iyayensa ke nan kuma yayi karatu a wata makaranta mai suna American International School of Lagos.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan Massad ne, mamallakin SCOA Najeriya kuma mahaifiyarsa mai suna Sarah ita ce ta kafa Society for Performing Arts in Nigeria.

An yi musu baiko da Tiffany, diyar Donald Trump mai shekaru 28 a Amurka a 2021.

Ya bukaci auren Tiffany da lu’u-lu’u mai nauyin carat 13 daga Dubai wanda darajarsa ta kai $1.2 miliyan.

Sama da baki 500 zasu halarci auren

Kamar yadda PageSix.com suka bayyana, auren zai samu baki sama da 500 kuma za a yi gagarumin shagalin da Donald da tsohuwar matarsa Marla Maples ne zasu jagoranta.

An tattaro cewa:

“Ana ta shiri gagarumi tare da kimtsa yadda lamarin zai kasance. Wannan babbar ranar Tiffany ce kuma za a zubar da kudi. Babban lamari za a gudanar kuma tilas ya Kayatar.”

Kara karanta wannan

Dattawan Yarbawa Sun Tsaida 'Dan Takaransu Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

Tsohon shugaban kasan Amurka, Donald Trump dai hamshakin mai arziki ne wanda kudinshi suka shahara sakamakon kadarorin da ya mallaka.

Sai dai a kwanakin baya mun ji cewa wata lauya Letitia James ta maka Donald Trump a gaban kotu kan zargin zuzuta dukiyarsa tare da karya kan arzikinsa duk da bai kai hakan ba.

Tace tsohon shugaban kasan Amurka ya mori alfarma kala kala saboda wannan karyar wanda suka hada sa inshora da basukan bankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng