Da Duminsa: Truss, Sabuwar Firayim Ministan Ingila Tayi Murabus

Da Duminsa: Truss, Sabuwar Firayim Ministan Ingila Tayi Murabus

  • Sabuwar firayim ministan Ingila, Liz Truss ta bayyana murabus dinta a ranar Alhamis a titin Downing dake Ingila
  • Truss ta bayyana cewa nauyin yayi mata yawa kuma ta gane cewa ba zata iya sauke shi ba, hakan yasa tayi murabus
  • A cewarta, zata cigaba da zama a kujerar har zuwa lokacin da za a zabi wani ya gaje ta kamar yadda ta bayyana Sarki

Firayim ministan Ingila, Liz Truss, a ranar Alhamis tayi murabus daga mukaminta kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Liz Truss
Da Duminsa: Truss, Sabuwar Firayim Ministan Ingila Tayi Murabus. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wannan murabus din ba zuwa ne kasa da watanni biyu da hawanta kujerar ta.

Truss wacce ta kwashe kwanaki 45 a ofis tace tayi murabus ne bayan mako daya da tayi neman wanda zai gaje ta.

Ta sanar da hukuncinta nayin murabus ne a ranar Alhamis a titin Downing.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na shiga ofis da niyyar tabbatar da mafi karancin haraji, cigaban tattalin arziki da zai amfani da ‘yancin Brexit.”

- Tace.

Ta kara da cewa:

“Na gane cewa, bayan an dora min nauyin, ba zan iya sauke shi ba ganin yadda jam’iyyar Conservative suka zabe ni. A don haka ne nayi magana da Mai Martaba Sarkin da ya sanar cewa zan yi murabus daga mukamin shugabancin jam’iyyar Conservative.
“A safiyar yau na gana da shugaban kwamitin 1922, Graham Brady. Mun amince cewa za a yi zaben shugaba wanda za a kammala cikin mako mai zuwa.
“Wannan zai sa mu iya sauke shirye-shiryenmu tare da kiyaye daidaituwar tattalin arziki da tsaron kasa. Zan kasnace firayim minista har sai an zabi wanda zai gaje ni.”

Firayim ministan tuni ta bayyana cewa tsananin wahalar aikin bayan wani babban minista yayi murabus.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Daga Hawa Mulki, Firayim Ministar Ingila ta ba ‘Yar asalin Najeriya Kujerar Minista

A wani labari na daban, Liz Truss ta bada sanarwar nada Misis Kemi Badenoch a matsayin Ministar kasuwanci da kasashen ketare na kasar Birtaniya.

Sanarwar sabuwar Firayim Ministar Ingila watau Liz Truss ta fito ne a shafin ofishin shugaban Ingila a Twitter a ranar 6 ga watan Satumba 2022.

Baya ga kujerar Ministar kasuwanci, Kemi Badenoch mai shekara 42 za ta jagoranci majalisar kasuwanci ta Birtaniyar a matsayin shugabanta.

Rahoton Channels TV ya nuna an haifi Badenoch ne a matsayin Olukemi Olufunto a Wimbledon da ke Landan, asalin iyayenta mutanen Najeriya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel