Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Aka Tsinci Jakar Wata Mata Da Ya Ɓace Shekaru 63 Da Suke Wuce, An Gano Mai Jakar

Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Aka Tsinci Jakar Wata Mata Da Ya Ɓace Shekaru 63 Da Suke Wuce, An Gano Mai Jakar

  • An gano wani jakar mata da ake ce ya bace shekaru 63 da suka shude a wani makaranta da ake kyautata zaton nan ya fadi
  • An gano cewa sunan mai jakar Beverly Williams wacce ta rasu a shekarar 2016, amma an gano yar ta
  • A cikin jakar, an gano kayayyakin Williams da hotonta a lokacin tana karamar yarinya

Amurka - An gano wani karamin jaka da ya bace a 1963 mallakar wata mata mai suna Beverly Williams a kasan wani makaranta a Texas.

An gano jakar ne kimanin shekaru 63 bayan ya bace a makarantar Clear Creek Independent School.

Lost purse
Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Aka Tsinci Jakar Wata Mata Da Ya Ɓace Shekaru 63 Da Suke Wuce, An Gano Mai Jakar. Hoto: KHOU
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

An gano yar matar da jakar na ta ya bace kuma za ta tafi ta karba nan ba da dade wa ba.

Abin bakin ciki, Beverly, ainihin mai jakar ta rasu a shekarar 2016 kafin a gano jakar a shekarar 2022.

An sanar da gano jakar ne a Instagram

A yayin da makarantar ta gano jakar, ta yi kokarin gano ainihin mai ita, har a Facebook an yi shela.

Mataimakiyar Shugaba, LCHS, Richard Lewis ta ce:

"Jakar na dauke da wani abu da ya yi kama da wallet, amma ashe littafin ajiye muhimman bayanai na yau da kullum ne (diary). Ana iya kwatanta shi da Facebook na yau: kana rubuta komai. Ta yi rubutu kan soyayyarta, wanda ta rabu da shi.
"Daya cikin hotunan na ta ne lokacin tana wata 9 da rabi kuma an rubuta 1946 a jikinsa, don haka za a iya kiyasta shekarunta sun kai 76.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da aka ga bidiyon mata mai juna biyu na leburanci a wurin wani gini

"Ita ce autar yayyinta mata uku. Mahaifiyarta ta rubuta sunanta Mrs Frank Williams, kuma muna da hoton mahaifin amma ba mu san sunanta na farko ba."

An tsinci jakar ne a ranar 5 ga watan Oktoba kuma yar matar ta yi mamakin jin labarin.

Dattijo Ɗan Shekara 74 Ya Yi Auren Farko A Wata Jihar Arewa, Ya Bayyana Dalilin Rashin Yin Aurensa Da Wuri

A wani rahoton, wani mutum mai shekara 74 daga Jihar Kogi mai suna Mallam Muhammad Awal, ya yi auren farko a rayuwarsa, rahoton LIB.

Awal ya aure wata bazawara mai shekara 45, Mallama Rahmat Muhammad, a Lokoja, babban birnin jihar Kogi a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta.

Da ya ke magana da manema labarai kan dalilin da yasa ya jinkirta yin aure, dattijon ya ce rashin kudi ne yasa bai nemi wata mace da aure ba.

Kara karanta wannan

An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164