Ba wai bane: Robert Mugabe yana da Digiri har da Di-gir-gir

Ba wai bane: Robert Mugabe yana da Digiri har da Di-gir-gir

- Robert Mugabe yana da Digiri rututu daga Jami’o’i da dama

- Mista Mugabe Malamin Makaranta ne kafin ya zama Shugaba

- Ana dai maganar Digirin shiga aji ne ba wai Digirin kyauta ba

Mun samu labari cewa tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe watau Robert Gabriel Mugabe yana cikin Shugabannin da su ka fi kowa karatun Boko a kaf tarihin Afrika da ma Duniya.

Ba wai bane: Robert Mugabe yana da Digiri har da Di-gir-gir
Tsohon Shugaban Kasa Mugabe yana da Digiri rututu

Robert Mugabe da yayi shekaru kusan 40 a mulki tsohon Malamin Makaranta ne kuma yayi karatun Digiri har 2 kan fannin shari’a a cikin gidan yari. Ya kuma yi Digirin sa na karshe lokacin ya karbi mulkin kasar su bayan samun ‘yancin kai.

KU KARANTA: Ko ka san Marigayi Alex Ekwume yana da Digiri har 6

Mugabe ya fara da Digiri a yaren Turanci a Jami’ar For Hare a 1951. Daga nan kuma yayi Digir wajen sanin harkar aikin ofis a Kasar Afrika ta Kudu. Mugabe kuma yana da Digiri a fagen koyarwa duk a wata Jami’a a Kasar ta Afrika ta Kudu.

Robert Mugabe ya kuma yi karatu a fannin tattalin arziki a Landan wanda bayan nan yayi Digiri na daya da biyu a harkar shari’a. A karshe Mugabe yayi karatun Digir-gir a harkar da ta shafi tattalin arziki duk a Kasar Ingila lokacin ya zama Shugaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng