Bidiyon Hirar Da Aka Yi Da Matar Da Ke Auren Maza 2, Ta Ce A Gado Ɗaya Suke Kwana Kuma Suna Zaman Lafiya

Bidiyon Hirar Da Aka Yi Da Matar Da Ke Auren Maza 2, Ta Ce A Gado Ɗaya Suke Kwana Kuma Suna Zaman Lafiya

  • Francine Jisele yar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, DRC, tana zaune tare da mazanta biyu; mijin farko Remi Murula da na biyu Albert Jarlace
  • Murula ya bar gida ya shiga duniya neman arziki kuma ya dena tuntubar matarsa, duk da cewa sun haifi yara biyu
  • Bayan ta dauki lokaci mai tsawo tana jiransa, Jisele ta yanke shawarar sake yin wani aure amma Murula ya dawo bayan shekara guda

DRC - Wata mata yar kasar Congo ta auri maza biyu hakan ya girgiza mutane, duba da cewa mata ba su cika yawan auren maza biyu a Afirka ba.

Mata mai maza biyu
Remi Murula, Francine Jisele da Albert Jarlace. Photos: Screengrabs from Afrimax English
Asali: UGC

A gida daya dukkansu ke zaune

Polyandry shine tsarin da mace ke auren maza biyu kuma dukkansu su rika zama a gida daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yadda na kwashe shekaru da dama ina jinyar mijina kan ciwon PTSD, Aisha Buhari

Francine Jisele tana zaune tare da mijinta na farko Murula da mijinta na biyu Albert Jarlace a gida daya tare da yaransu.

Jisele ta auri Murula shekaru shida da suka shude kuma sun kaifi yara biyu. Ya shiga duniya neman arziki kuma ya dena mata sako ko waya.

Ta fada wa Afrimax English a wani hira cewa:

"Saboda wahalhalun rayuwa, mutumin ya yi tafi kuma bai dawo ba. Na tsinci kai na cikin kadaici, na shafe shekaru uku da rabi ni kadai ba tare da miji ba."

Mijin ta na farko ya dawo

Ta bayyana cewa:

"Bayan wannan shekarun na rasa shi kuma na fara soyayya da wani mutum. Bayan shekara daya, mijin na farko ya dawo."

Jisele ta ce ba ta yi tsamanin mijinta na farko zai dawo ba bayan shekarun nan masu yawa.

Albert Jarlace ya ce:

"Na hadu da wannan matar lokacin da na ke aiki a ma'aikatar hakar ma'adinai kuma ta fada min tana da wani miji da yadda ya bar ta ya tafi duniya don neman rayuwa."

Kara karanta wannan

Matar Aure Dake Zama Gida Daya da Mijinta da Saurayinta Tace Duniya Tayi mata Dadi

Ya kara da cewa:

"Na ga kaman ba ni da zabi saboda muna tare kuma na zauna da ita ba tare da sanin tana da wani miji ba."

Da Murula ya dawo ya yi fada da Jarlace yana cewa Jisele matarsa ce

Jarlace ya ce:

"Matar ta ce kada in rabu da ita. Don haka na ga ya dace in tsaya da ita yanzu kuma mun haifi yaro daya."

Murula ya kara da cewa:

"Tuko watatu (maza biyu ne ke nan). Ba mu da matsala, wannan matar mu ne. Tunda na bar gida ban yi magana da matata ba ko sau daya. Da na dawo, na tarar da ita tare da wani mutum."

Murula ya bukaci Jarlace ya tafi

Da farko, Murula ya bukaci Jarlace ya tafi amma ya ce babu inda zai tafi.

Ya ce:

"Da farko na rika hayaniya amma na duba cewa matata ta aikata hakan ne don tunda na tafi bata ji daga gare ni ba. Ba ni da wurin zuwa don haka laifi na ne."

Kara karanta wannan

Kuna bata lokacin ku ne: Fasto ya ce Allah ya nuna mashi wanda zai lashe zaben 2023

Jisele ya ce:

"A kwano daya muke cin abinci, a daki daya muke barci a gado daya. Ina son su dukkansu. Muna zaman lafiya a gida."

Matar ce bayyana wanene mahaifin yara

Idan an zo wurin kwanciya, daya cikinmu zai bar daya. Matar ce ke bayyana mahaifin yara.

Murula ya ce:

"Yan uwana sun san halin da na ke ciki amma suka shawarci in kwantar da hankali na domin ni ne na tafi na bar matata."

Jisele ta ce abin ba sauki, ta so a ce kowannensu na da gida kuma sai ta rika zuwa gidan. Ba ta son su uku su rika haduwa a daki daya yayin barci.

Jarlace ya ce:

"Ina son in tafi in ba su wuri domin shine 'sanannen mijin matar'. Idan zan iya samun taimakon tikiti zan tafi in bar dayan mijin ya zauna a gidan. Matar ba ta amince in tafi ba."

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

"Ba na jin dadin yadda mu biyu ke auren mata daya; filin da gidan nawa ne kuma matar nawa ne."

A halin yanzu, Murula ya ce su ukun za su cigaba da zama tare har sai daya ya gaji ya tafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164