Pantami Ya Jagoranci Najeriya da Afrika Sun Samu Gagarumar Nasara a Duniya
- Najeriya ta kuma shiga cikin ‘yan kungiyar International Telecommunications Union na Duniya
- Kasar Afrikan ta samu wannan dama ne a zaben da aka gudanar a birnin Budapest a Romania
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya jagoranci Najeriya ta bada tazarar da ba a taba gani a ITU ba
Romania - A taron kungiyar ITU na Duniya, mun samu labari cewa Najeriya ta samu gagarumar nasarar sake shiga cikin majalisar kungiyar.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na kasar nan, Isa Ali Ibrahim Pantami ya bada sanarwa Najeriya tayi nasara a zaben da aka yi,
Da yake magana a shafinsa a ranar Litinin, 3 ga watan Oktoba 2022, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami yace Najeriya ta lashe kuri’u da yawa.
Ko da yake bai yi bayanin yadda sakamakon zaben ya kasance ba, amma Ministan tarayyan yace kasarsa ta bada tazaran da ba a saba gani ba.
ITU kungiya ce ta harkar sadarwa na Duniya wanda Najeriya take cikinta. Kafin kasa ta iya shiga cikin ITU sai an yi zabe bayan shekaru hudu.
A Nuwamba ne wa’adin kasashen Afrika 12 da ke kungiyar zai kare don haka aka shirya zabe a taron da ake yi a Bucharest a kasar Romania.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Pantami ya taimaki Afrika
@ProfIsaPantami shi ne wanda ya kada kuri’a a zabukan da aka yi a madadin mutanen Najeriya.
SwiftReporters tace Mai girma Ministan ya nuna jagoranci da ya bada gudumuwa wajen ganin Dr. Cosmas Zavazava ya zama Darekta a ITU.
Gudumuwar Ministan kasar ta taimaka wajen nasarar da Dr. Cosmas Zavazava na Zimbabwe ya samu a matsayin darektan bangaren cigaba.
Taron ITU ya yi armashi
A taron da ake yi tun karshen watan Satumba, Isa Pantami ya halarci zama da shugabannin ITU na Ingila, Amurka, Switzerland da na Sin.
Sannan Ministan mai shekara 49 ya yi jawabi a kan damfara ta yanar gizo a birnin Bucharest, kuma ya halarci liyafar da Saudi Arabia ta shirya.
Minista yana ganin barazana
Kuna da labari Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya shigo da tsarin yin rajistar NIN a wayoyin salula a shekarar 2021 domin a inganta harkar tsaro.
Amma wannan mataki da Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin kasar ya dauka, ya zo da irin farashinsa, ta kai wasu na neman kashe hi.
Asali: Legit.ng