Yarima Ibn Salman ya zama Firayim Ministan Saudi, ya karbi mukamin Mahaifinsa

Yarima Ibn Salman ya zama Firayim Ministan Saudi, ya karbi mukamin Mahaifinsa

  • Gwamnatin Saudi tayi wani canje-canjen Ministoci, Mohammed bin Salman ya zama Firayim Minista
  • Hukumar dillacin labaran kasar Saudi Arabiya ta tabbatar da wannan sanarwa a yammacin a makon nan
  • Ibn Salman ya dare kujerar Mahaifinsa mai shekara 86, kaninsa ya karbi mukaminin Ministan tsaro

Saudi - Yarima mai jiran gado a kasar Saudi Arabiya, Mohammed bin Salman ya zama sabon Firayim Minista a canjin Ministoci da aka yi.

Gwamnatin Saudi Arabiya ta tabbatar da wannan sauye-sauye da aka yi a gwamnati ta bakin hukumar dillacin labaran kasar a yammacin Talata.

Kamar yadda bayanin da aka wallafa a shafin SPA na Twitter ya nuna, Ibn Salman ya zama Firayim Minista, ya bar kujerarsa na Ministan tsaro.

Kafin zamansa Firayim Minista, Mohammed bin Salman wanda aka sani da MBS shi ne mataimakin Firayim Minista kuma babban Ministan tsaro.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban Matasan Arewa Da Ya Taka Rawar Gani Don Nasarar Buhari A 2015 Ya Fita Daga APC Ya Koma Labour Party

Khalid bin Salman ya zama babban Minista

Yanzu an maye gurbinsa na Ministan harkokin tsaro da kaninsa, Khalid bin Salman wanda shi ne Mataimakin Ministan a ma’aikatar kafin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

France 24 tace kusan dai Yariman ne yake juya akalar gwamnatin Saudiyya, wannan mukami da ya samu ya tabbatar da matsayinsa a hukumance.

Yarima Ibn Salman
Mohammed bin Salman da Sarki Salman Abdulaziz Hoto: www.middleeastmonitor.com
Asali: UGC

Tasirin Yarima a Saudi

Masu fashin baki sun nuna cewa Sarki Salman mai shekara 86 yana mikawa babban ‘dansa ragamar mulkin kasar Larabawan ne sannu a hankali.

Tun kafin yanzu, Ibn Salman mai shekara 37 a Duniya shi ne ke da ta-cewa wajen abubuwan da suka shafi tattali, tsaro, mai da yake-yaken Saudiyya.

Sanarwar tace Sarkin zai cigaba da gudanar da harkokin gwamnati a matsayinsa na Shugaba, shi ne zai rika jagorantar majalisar Ministocin kasar.

Canjin Minitocin gwamnati

Aljazeera tace manyan Ministoci sun rike mukamansu. Daga ciki akwai Faisal bin Farhan Al Saud, Mohammed al-Jadaan da kuma Khalid al-Falih.

Kara karanta wannan

'Dan takaran 2023 Ya yi Sabon Zama da Obasanjo, An yi Kus-kus 'a kan batun kasa'

A sanadiyyar wannan canji ne aka nada sabon Ministan harkokin hajji da umrah. Tawfiq bin Fawzan bin Mohammed Al-Rabiah zai rike ma'aikatar.

Zabe a Najeriya

Kun samu rahoto nan da ‘yan watanni ‘Yan Najeriya za su samu kansu wajen kada kuri’u a zaben sabon shugaban kasa a karo na bakwai daga 1999.

Mun fahimci cewa za ayi amfani da dukiya, kabilanci da sabanin addini wajen karkato da hankalin masu kada kuri’a a zaben sabon shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng