Sai Da Aka Kwabe Ni: Wata Budurwa Ta Bayyana Alhininta Na Kulla Soyayya Da Dan Najeriya

Sai Da Aka Kwabe Ni: Wata Budurwa Ta Bayyana Alhininta Na Kulla Soyayya Da Dan Najeriya

  • Wata budurwa yar kasar Kenya ta bayyana yadda iyaye a kasar ke gargadin yaransu mata kan soyayya da yan Afrika ta yamma
  • Huddah Monroe ta ce musamman iyaye kan ja kunnen 'ya'yansu mata kan kulla alaka da mazan Najeriya
  • Ta ce ko ita sai da mahaifiyarta da goggwaninta suka zaunar da ita tare da kwabarta kan haka amma bata ji ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kenya - Wata matashiyar budurwa yar kasar Kenya mai suna, Huddah Monroe, ta nuna nadamarta na kin bin maganar mahaifiyarta da goggwaninta.

Monroe ta ce mahaifan nata sun kwabeta a kan soyayya da mazan Afrika ta yamma musamman ma mazan Najeriya amma ta ki ji.

Shafin LIB ya rahoto cewa budurwar ta bayyana hakan ne yayin da take tuna lokacin da shugaban kasar Kenya, William Ruto ya yarda cewa mawuyacin abu ne gare shi aurar da diyarsa ga dan Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda 'yar Najeriya ta shiga tashin hankali bayan yiwa sarauniyar Ingila mummunan fata

Huddah
Mahaifiyata Ta Gargadeni Game Da Soyayya Da Yan Afrika Ta Yamma Musamman Mazan Najeriya – Budurwa Yar Kenya Hoto: @huddahthebosschick
Asali: Instagram

Ta kuma jadadda cewa dukkan iyaye a kasar su kan gargadi 'ya'yansu mata kan haka da zaran sun fara balaga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

“A kasar Kenya, kowasu iyaye suna jan kunnen yaransu mata kan mazan Afrika ta yamma da zaran alamar girma ya fara bayyana a kirjinmu. Bama jin magana.
“A lokacin da nake matashiyar budurwa, mahaifiyata da goggwanina suna fada mani cewa kada na kuskura nayi soyayya da mutumin Afrika ta yamma, musamman mazan Kongo da Najeria. Naso ace na saurare su, ban san da haka ba sai yanzu.”

Bidiyo: Budurwar Da Ta Rabu Da Saurayinta Talaka Saboda Mai Kudi Ta Koka, Bata Auru Ba Bayan Shekaru 10

A wani labarin, wani bidiyo mai tsawon sakanni 56 a TikTok ya nuno wata matashiyar budurwa wacce tace shekarunta 40 amma har yanzu bata da aure.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

A cewar budurwar, wani saurayi mai dattako ya nemi aurenta shekaru 10 da suka gabata amma sai daga bisani ta soke shirye-shiryen auren ana saura sati biyu.

Ta tuna yadda ta soke auren saboda ta samu wani saurayi mai kudi wanda take tunanin zai aure ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel