An Tono Jerin Tarin Dukiya da Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bari a Duniya

An Tono Jerin Tarin Dukiya da Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bari a Duniya

  • Sarauniya Elizabeth II ta mutu ta bar kudi masu yawan gaske, da kayan ado, da dukiyoyi iri-iri a Duniya
  • A duk shekara, Gwamnatin Birtaniya tana warewa Sarauniya da fadarta makudan miliyoyi domin kula da ita
  • Rahotanni sun ce Marigayiyar ta bar wa magajinta watau Sarki Charles III gadon $70m da wasu kadarorin

United Kingdom - A ranar Alhamis da ta gabata Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta bar Duniya. Elizabeth ta cika tana shekara 96, tayi shekaru 70 a mulki.

Rahoton da muka samu daga Fortunes yace abin da Elizabeth II ta mallaka na fada da danginta ne. Haka abin yake tun zamanin Mai martaba George VI.

Bayan shekaru 70 a mulki, dukiyar da Sarauniya ta bari a Duniya ya zarce Dala miliyan 500. Sarki Charles III zai gaje mafi yawan abin da aka bari.

Kara karanta wannan

Tsohon Tarihi: Yadda Elizabeth II Ta Takawa Buhari Burki Shekaru 38 da Suka Wuce

Tun zamanin Sarki George III aka daina biyan Sarakunan Ingila albashin majalisa a kowane wata, suna karbar kudi ne duk shekara daga kasafin Birtaniya.

A 2012 aka ware $86m a cikin wani asusun kudi na musamman, da su aka rika yi wa Sarauniya dawainiyar duk abin da ya shafi kula da zirga-zirgarta.

Fadar Sarakunan Birtaniya

Kamar yadda muka samu labari daga Forbes, darajar fadar Sarkin na Ingila ta kai Dala biliyan 28 a yau, kuma babu wani wanda ya isa ya saida komai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Queen Elizabeth II
Sarauniya Elizabeth II Hoto: fortune.com
Asali: Getty Images

Wasu daga cikin kadarori:

Gidajen Crown Estate: $19.5bn

Fadar Buckingham: $4.9bn

Kasar Cornwall: $1.3bn

Kasar Lancaster: $748m

Fadar Kensington: $630m

Gidajen Scotland: $592m

Akwai wasu kadarorin kamar The Crown Estate da The Privy Purse wanda sun fi shekara 600.

Nawa Elizabeth ta ke da shi?

Business Insider ta rahoto cewa Sarauniyar da ta rasu, ta mallaki sama da Dala miliyan 500 na kan ta saboda kayan ado, gwala-gwalai, da gidajenta.

Kara karanta wannan

Wakokin Sabawa Koyawar Addini Da Al'adu: Jerin Sunayen Mutum 10 Da Kotun Kano Tayi Umurnin A Kama

Baya ga haka, ta gaji $70m daga wajen mahafiyarta a shekarar 2002. A lokacin ne ta samu kayan ado, dawakan alfarma da hannun jari a kamfanoni.

Fadar Sarki a Ingila

Wani rubutu da aka yi a jaridar 21st Century Chronicle ya nuna cewa a cikin fadar Buckingham akwai katafaren dakuna fiye da 200 da ban daki kusan 80.

Akwai dakuna 188 da ofisoshi 92 da aka ware domin ma’aikatan da ke aiki a fadar Ingilar. An yi lokacin da akwai mutane har 700 da ke taya Sarauniya aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng