Sanata Ekweremadu ya ga ta kan shi a Kotu, an hana shi beli, Alkali ya saki Mai dakinsa

Sanata Ekweremadu ya ga ta kan shi a Kotu, an hana shi beli, Alkali ya saki Mai dakinsa

  • Bayan watanni biyu a tsare, Alkali ya bada belin Beatrice Ekweremadu mai shekara 55 a Duniya
  • Kotun Birtaniya ta amince ta saki Beatrice Ekweremadu ne amma tattare da sharuda masu tsauri
  • Amma har yanzu Sanata Ekweremadu yana gidan maza, kotu ba za ta sake zama ba sai a makon gobe

England - Beatrice Ekweremadu ta na fuskantar shari’a a kotun Birtaniya tare da mai gidanta, Sanata Ike Ekweremadu wanda ‘dan siyasa ne a Najeriya.

Labarin da muka samu a safiyar Talata, 26 ga watan Yuli 2022 shi ne Alkali ya bada belin Beatrice Ekweremadu, za ta bar hannun 'yan sandan Birtaniya

Ana tuhumar tsohon mataimakin shugaban majalisar Najeriya da mai dakinsa da zargin kinkimo karamin yaro zuwa Ingila domin amfani da kodarsa.

Duk da kotu ta amice a bada belin Beatrice Ekweremadu, mai gidanta Sanata Ike Ekweremadu bai yi irin sa’ar da tayi ba, zai cigaba da zama a daure.

Kara karanta wannan

Na kadu: An kashe dan uwan shugaban PDP, Buhari ya sha alwashin daukar mataki, ya kakkausan martani

Ike Ekweremadu wanda shi karon kansa lauya ne zai amsa zargin dauko ‘dan shekara 21 daga Najeriya zuwa Landan domin a cire kodar da ta ke jikinsa.

Sanatan na yammacin jihar Enugu yana neman ayi amfani da kodar wannan Bawan Allah, a dasawa wata diyarsa mai fama da larura, ta na gadon asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ekweremadu
Sanata Ike Ekweremadu Hoto: @iamekweremadu
Asali: Twitter

Daily Mail ta ce a ranar Juma’ar da ta wuce wadannan ma’auratan Najeriya suka koma gaban kotun na kasar Birtaniya domin cigaba da zaman shari'a.

An bada belin Beatrice Ekweremadu

Alkali Richard Marks ya amince a bada belin Beatrice Ekweremadu kamar yadda ta nema.

“Matsayinmu shi ne na bada beli ga Beatrice, tattare da wasu tsauraran sharuda, amma na ki amincewa in bada belin Ike (Ekweremadu).

Rahoton This Day ya nuna cewa lauyoyin gwamnati ba su kalubalanci hukuncin da Alkali ya zartar da aka zauna domin sauraron karar a makon jiya ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Lauyan da ya shigar da kara, Tim Probert-Wood yace wadannan ma’aurata za su amsa laifin neman amfani da gabban mutum, ta hanyar sabawa doka.

A ranar 4 ga watan Agustan 2022 za a koma kotu domin cigaba da shari’a. Tun watan Mayu aka kama su Ekweremadu bayan isowarsu daga Turkiyya.

An kai APC kotun Abuja

Dazu an ji labari wani Lauya, Osigwe Momoh yana kalubalantar tikitin Musulmi da Musulmi a kotu, yana iya kawowa takarar APC a zaben 2023 barazana.

Barista Osigwe Momoh yace dokar kasa ba ta halastawa Bola Tinubu dauko wani Musulmi ya zama abokin takararsa ba, ya roki a hana APC shiga takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng