Direban Tasi da ya Mayar da N438k da Aka Manta a Motarsa ya Samu Babban Aiki, Ya Bayyana Hotuna

Direban Tasi da ya Mayar da N438k da Aka Manta a Motarsa ya Samu Babban Aiki, Ya Bayyana Hotuna

  • Direban tasi da ya mayarwa fasinja N438k da aka bari a motarsa ya samu aiki a hedkwatar cocin Pentecost dake Accra a kasar Ghana
  • Kwesi Ackon ya tsinta kudin wata 'yar kasuwar da ta bar su a motarsa bayan ya sauke ta a gidanta dake Teshie a ranar Asabar
  • Bayan ya mayar da kudin, ya samu kyautuka daban-daban daga jama'a har da N1m daga mataimakin shugaban kasar Ghana

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Accra, Ghana - Kwesi Ackon, direban tasin da ya mayarwa wata fasinja kudi har N438k da ta bari a motarsa, yanzu ya samu aiki a hedkwatar cocin Pentecost dake Accra, Ghana.

Direban mai shekaru 36 wanda ke zuwa cocin Onyeametease a yankin Kokomlemle dake kasar, ya fara aikin a ranar Alhamis, 16 ga watan Yunin 2022.

Kwesi Ackon, Direban Tasi Mia Gaskiya
Direban Tasi da ya Mayar da N438k da Aka Manta a Motarsa ya Samu Babban Aiki, Ya Bayyana Hotuna. Hoto daga @_gustavo400/@thepressradio
Asali: Twitter

Ackon ya bayyana godiyarsa ga Ubangiji da cocin kan aikin da suka bashi, Graphic Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

Ya kara mika godiyarsa ga 'yan kasar Ghana wadanda suka bashi kyautar kudade da kayayyaki bayan labarin gaskiyarsa da rikon amana sun zagaye kafafen sada zumuntar zamani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda al'amarin ya faru

Ackon ya dauka wata mai siyar da kifi daga kasuwar Mallam Atta a Accra zuwa gidanta dake Teshie a ranar Asabar din Easter.

'Yar kasuwar ta manta da N438k a motarsa amma ya mayar mata da kudinta. Wannan gaskiyar da ya nuna ya janyo masa maganganu daga kafar sada zumunta inda wasu ke son kara sanin waye Kwesi.

Bayan wannan kyautatawar, direban tasin ya samu kyautar kudade daga kungiyoyi daban-daban da mutane har da mataimakin shugaban kasa Dr Mahamudu Bawumia wanda ya gwangwaje shi da Naira miliyan daya.

Bidiyon Yadda Mai Kwalliya Ya Maida Tsohuwa Zuwa Zukekiyar, Farar, Matashiyar Budurwa

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku: 'Zunuban' Wike, Dalilan Da Yasa Aka Zabi Okowa, Majiya Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

A wani labari na daban, mutane ba za su gaji da magantuwa a kan mai kwalliyar da ya sauya halittar wata mata gaba daya ba.

Wani bidiyo da ya yi yawo ya tada kura a kafafan sada zumuntar zamani. A bidiyon TikTok din, an ga yadda wata mata mai kwarmin ido ta zauna gami da mika fuskarta ga wani mai kwalliya don ya yi aiki a fuskarta.

Mutane da dama sun yi mamakin yadda matar ta koma bayan an kammala kwalliyar. Gaba daya kwalliyar, wacce ta dauki tsawon lokaci ana yi, a yanke ta zuwa sawu sakonni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel