Matata Da ƳaƳana Sun Saba Haɗuwa Su Lakaɗa Min Duka, Magidanci Mai Neman Saki

Matata Da ƳaƳana Sun Saba Haɗuwa Su Lakaɗa Min Duka, Magidanci Mai Neman Saki

  • Wani magidanci a Legas ya yi karar matarsa a kotu yana neman a datse igiyar auren da ke tsakaninsu bayan shekaru 36
  • Kazeem Ogidan, tsohon ma'aikacin banki mai shekaru 62 ya yi zargin cewa matarsa da yayansa duk dukansa suke yi kuma suna barazanar halaka shi
  • A bangarenta, matarsa, Risikat ta shaida wa kotu cewa shine baya taba bari ta samu kwanciyar hankali kuma yayansa sun taso sun ga yana dukanta ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Wani tsohon ma'aikacin banki, Mr Kazeem Ogidan, a ranar Laraba ya nemi a raba aurensa na shekaru 36 da matarsa Risikat a wata kotun kwastamare da ke Ikorodu, Legas.

A korafinsa, Ogidan, ya yi zargin cewa matarsa tana dukansa, rahoton NAN.

Matata Da ƳaƳana Sun Saba Haɗuwa Su Lakaɗa Min Duka, Magidanci Mai Neman Saki
Matata Da ƳaƳana Suna Lakaɗa Min Duka, Magidanci Mai Neman Saki. Hoto: NAN.
Asali: Twitter

Ogidan, wanda ke zaune a Lowcost Estate a Ikorodu, ya roki kotun ta raba aurensa da matarsa.

Kara karanta wannan

Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Matata tana duka na, ta kuma zuga yayan mu hudu su rika min duka. Da na na farko ya yi barazanar saka min guda a abin ci.
"Dan mu na uku ya yi barazanar zai caka min wuka. Kullum hada baki suke yi don cutar da ni," in ji shi.

Matar ta musanta abin da mijinta ya fada

Amma, Risikat, mai shekaru 58, kuma yar kasuwa, ta musanta abin da mijinta ya fada, ta yi zargin cewa baya faranta mata rai, kamar yadda The Nation ta rahoto.

"Kullum miji na fada ya ke yi da ni. Ba ni da kwanciyar hankli.
"Yara na sun girma suna kallon miji na yana duka na. Sun yi kokarin su kare ni.
"Ba su taba dukansa ba," in ji ta.

Alkalin kotun, Mrs Saadat Quadri, ta yi yara biyu tambaya kan zargin da mahaifinsu ya yi a kansu.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Ta daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Mayun 2022.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel