Shugaban Makaranta Ta Siya Wa Ɗalibai Da Ke Sallah a Ban Ɗaki Dadduma, Ta Kuma Tanada Musu Sabon Wurin Sallah

Shugaban Makaranta Ta Siya Wa Ɗalibai Da Ke Sallah a Ban Ɗaki Dadduma, Ta Kuma Tanada Musu Sabon Wurin Sallah

  • Wata makarantar Sakandare da ke Derby a Birtaniya ta siyo daddumai kuma ta samar da wuri na musamman don bai wa dalibai musulmai damar yin sallah a tsanake
  • Hakan ya biyo bayan yadda shugaban makarantar ta gano ana tilasta su yin sallolin ko wacce rana a cikin ban dakin makarantar saboda ba su da wurin yin ibada
  • Shugaban makarantar Alvaston Moor, Michelle Strong ta ce an tanadi daddumomi sallah ne saboda ganin muhimmancin addini da al’adar ko wanne dalibi kasancewar su na yin bikin Kirsimeti

Birtaniya - Wata makaranta da ke Derby a Birtaniya ta tanadar da bangare na musamman wanda dalibai musulmai za su dinga yin sallah a ko wacce rana cikin tsanaki bayan shugabar makarantar ta gano ana tilasta musu yin sallah a cikin makewayar makarantar.

Kara karanta wannan

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Michelle Strong, shugabar makarantar Albaston Moor ta ce ta dauki matakin siyan akwati biyu cike da daddumai ne bayan ta gano akwai dalibai musulmai a makarantar, Derby Telegraph ta rahoto.

An tanadar wa musulmi da ke sallah a ban ɗaki dadduma da wurin yin sallah a wata makaranta a Birtaniya
An tanadar wa musulman Turai masu sallah a bayi isasshen wurin yin ibadarsu. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Ta bukaci su dinga shimfida dadduman ne a dakunan karatu lokacin cin abincin rana inda ta ware bangare na musamman wanda za su dinga yin sallolinsu. Wani lokacin idan dakin karatun ya cika da jama’a, ana samar musu wani dakin na daban don su yi salloli a natse.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabar makarantar ta nuna muhimmancin ko wanne addini

Kamar yadda Daily Trust ta nuna, Mrs Strong wacce ta hau kujerar shugabancin makarantar Alvaston Moor mai dalibai 850 a watan Satumban 2021, ta ce:

“Mun siyo daddumai saboda gane muhimmancin ko wacce al’ada. Makarantarmu cakudaddiya ce. Don haka wajibi ne mu fahimci muhimmancin ko wacce al’adar daliban da mu ke da su a makarantar. Har bikin Kirsimeti mu na yi.

Kara karanta wannan

Fashewar tukunyar gas a Kano: Harkoki sun daidaita amma iyaye sun ki mayar da yaransu makaranta

“Ya kamata ace makaranta ta kasance wuri mai tsanaki wanda kowa zai yi rayuwarsa da kuma addininsa ba tare da fargaba ba.
“Dalibanmu musulmai su na ta murnar ganin sabbin dadduman. Ina fatan hakan zai faranta musu rai kuma su gane cewa mutane sun fahimci yadda addininsu ya ke.”

Daliban makarantar sun nuna farin cikinsu akan lamarin

Ruhaan Rizwan, dalibi ne da ke aji na 8 a makarantar Alvaston Moor, daya daga cikin dalibai musulmai masu amfani da dadduman da rana don yin sallah.

Ruhaan ya yaba wa Mrs Strong da kuma mai kula da dakin karatun Brackens Lane na makarantar, Amber Fletcher, akan siyan daddumai da kuma samar da bangare na daban a cikin dakin karatun makarantar don musulmai su dinga yin sallah.

A cewarsa:

“Mrs Strong da Mrs Fletcher sun kasance masu girmama jama’a. Na yi matukar jin dadin hakan. Ina ganin makarantar ma ta karrama mu. Ina godiya kwarai. Ba zan iya misalta irin farin cikin da na ke ciki ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel