Fashewar tukunyar gas a Kano: Harkoki sun daidaita amma iyaye sun ki mayar da yaransu makaranta

Fashewar tukunyar gas a Kano: Harkoki sun daidaita amma iyaye sun ki mayar da yaransu makaranta

  • Bayan fashewar tulun gas a yankin Sabon Gari da ke karamar hukumar Fage ta jihar Kano a ranar Talata, a yanzu harkoki sun koma daidai
  • Sai dai kuma yayin da shaguna suka bude, makarantu sun ci gaba da kasancewa a kulle saboda iyaye sun yarda 'ya'yansu su koma ajujuwansu
  • An tattaro cewa har yanzu iyayen na cikin zullumi tun bayan da suka ji rade-radin wai dan kunar bakin waje ne ya tayar da bam

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Harkoki sun dawo hanyar Aba da ke yankin Sabon Gari ta jihar Kano wajen da tukunyar gas ta fashe tare da kashe mutane tara da jikkata wasu da dama a ranar Talata.

Sai dai kuma yawancin makarantu a yankin suna kulle yayin da iyaye suka ki bari yaransu su bar gidajensu sabosa ana ta rade-radin cewa dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

Fashewar tukunyar gas a Kano: Harkoki sun daidaita amma iyaye sun ki mayar da yaransu makaranta
Fashewar tukunyar gas a Kano: Harkoki sun daidaita amma iyaye sun ki mayar da yaransu makaranta Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Jaridar ta rahoto cewa a lokacin da wakilinta ya ziyarci wajen, ya lura cewa an bude wasu shaguna da wuraren kasuwanci, amma makarantu da ke da nasaba da wajen da abun fashewar ya tashi basu bude ba.

Baya ga makarantun, dukkanin shagunan da ke kusa da wajen sun ki budewa duk da cewar mummunan lamarin bai taba su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai shago a gefen wajen wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ekenna ya ce ya bude kasuwancinsa a ranar Laraba saboda abubuwa sun yi sauki.

Peter Udoko, wani mazaunin yankin kuma mai shago a wajen, ya ce diyarsa na a makarantar Winners Kid Academy lokacin da abun ya faru amma cewa Allah ya tsare ta.

Malam Ibrahim Dawakin Tofa, wani makusancin Vicent Ejike, mai aikin walda da ya mutu a lamarin, ya ce sun yi magana yan mintoci kadan kafin faruwar abin.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Tofa ya ce:

“Na wuce wajen sannan na fada mashi cewa zan dawo nan ba da dadewa ba. Abun takaici, ban dawo na same shi ba. Abun bakin ciki ne.”

Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

A baya mun ji cewa gwamnatin Jihar Kano, a ranar Talata ta ce ba a makaranta ne fashewar tulun gas ya faru a Sabon Garin Kano ba, The Nation ta rahoto.

Kwamishinan Labarai, Malam Muhammad Garba, wanda ya yi karin hasken ya ce fashewar ya faru ne a wani wurin ajiye abincin dabobbi 'da ke kallon makarantar' a Aba Road, Sabon Gari, karamar hukumar Fagge.

The Nation ta tattaro cewa wasu na fargabar cewa yan ta'adda sun fara kai hari makarantu a Kano bayan abin da ya faru a kusa da makarantar Winners Kid Academy.

Asali: Legit.ng

Online view pixel