Kyawawan hotunan 'dan tsohon gwamna yana mika bukatar aure ga budurwarsa

Kyawawan hotunan 'dan tsohon gwamna yana mika bukatar aure ga budurwarsa

  • Daga karshe, 'dan tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel, Adebola ya nemi budurwarsa ta zama matarsa ta har abada
  • Amaryar, Morenike, ta wallafa tsula-tsulan hotunansu a shafinta na Instagram, inda mabiyan Adebola Morenike suka cika sashin tsokaci da sakonnin taya murna
  • Inda wasu ke kokarin tuna sau nawa Adebola ya bukaci hakan daga gareta, na zama matarsa ta har abada

Ogun - Adebola Daniel, 'da ga tsohon gwamnan jihar Ogun ya shirya angwancewa da budurwarsa, Morenike, duba da yadda kwanan nan ya bukaci ta auresa, inda ta amince.

Da alamu neman auren ya faru ne a bainar 'yan uwa da abokan arziki, yayin da amaryar ta wallafa hotunan lokacin da hakan ya faru a shafinta na Instagram.

Kyawawan hotunan 'dan tsohon gwamna yana mika bukatar aure ga budurwarsa
Kyawawan hotunan 'dan tsohon gwamna yana mika bukatar aure ga budurwarsa. Hotodaga @mas_reiny
Asali: Instagram

Haka zalika, Morenike ta kara da bayyana yadda take matukar kaunar mijin da zata aura, irin soyayyar da suke wa juna da kuma yadda ta zabe shi fiye da kowanne 'da namiji.

Kara karanta wannan

A karon farko, Jaruma Hadiza Gabon tayi martani ga masu cewa tana kyautar Riya

"Ka shigo rayuwata, gami da nuna min duk abunda nake bukata, amma ban san yadda zan nema ba. Ka cika gurbin rayuwata, tare da ba wa rayuwata cikakkiyar ma'ana.
"Kai ne mutumin da yafi dacewa da ni. Kuma yafi dacewa da in hada zuri'a da shi. Da zoben da yafi dacewa. Ina kaunarka Adebola Daniel, daga yanzu na zabi in yi rayuwa da kai har abada. Ina matukar godiya ga duka wanda ya taya mu murnar soyayyarmu." a cewar amaryar.

'Yan Najeriya sun yi martani

souveniretc: "Sak mahaifinsa, ina taya ango da amaryar murna."
pretier_rolake: "Akwai yuwuwar wannan ne karo na uku da ya nemi ta auresa."
deborahfziba: " Ina taya ku muran gaba dayanku. Wannan ya sanya ni murmushi>"

Hotuna: Tsohon gwamna kuma dan takarar shugaban kasa ya aurar da diya

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja

A wani labari na daban, a cikin ranakun karshen mako, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban cin kasa, Peter Obi, ya aurar da diyarsa mai suna Gabriella ga masoyinta, Chukwuma Okeke-Ojiudu.

Shagalin auren wanda aka yi a Agulu, jihar Anambra, ya samu halartar manyan 'yan siyasa da suka hada da tsohon gwamnan Anambra, Dr. Chris Ngige, tsohon gwamnan Abia, T A Orji, Sanata Uche Ekwunife, tsohon gwamnan IMO, Emeka Ihedioha, mamallakin Innoson Group of Companies, Innocent Chukwuma, Chief Victor Umeh, tsohon dan takarar gwamnan Anambra, Oseloka Henry Obaze da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel