Yakin Ukraine da Rasha: Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea
- Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kakaba takunkumi kan gwamnatin Putin da magoya bayansa, Burtaniya ta sake daukar mataki
- Ta sanya takunkumi kan mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tare da bayyana shi a matsayin dan tsagin Putin
- Wannan na zuwa ne lokacin da kasar Ukraine ke ci gaba da fuskantar hare-haren bama-bamai daga kasar Rasha
Kasar Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallaon kafa ta Chelsea Roman Abramovich, kana ta sanya haramcin mu'amala da daidaikun mutane da 'yan kasuwa na Burtaniya, da dokar hana zirga-zirga duk dai akansa.
Sky Sports ta rahoto Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson yana cewa:
"Ba zai yiwu a samar da mafaka ga wadanda suka goyi bayan mummunan harin da Putin ya kai wa Ukraine ba."
Wani daftarin gidan gwamnati da aka fitar a ranar Alhamis ya ce Abramovich yana da "dangantaka ta kud da kud ta tsawon shekaru" da shugaban Rasha, Vladimir Putin, inji rahoton The Athletic.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazalika, ya kara da cewa:
"Takunkumin na yau shine mataki na baya-bayan nan na goyon bayan da Birtaniya ke baiwa al'ummar Ukraine ba tare da kakkautawa ba.
"Ba za mu sassauta ba wajen kuntatawa wadanda suka taimaka wajen kashe fararen hula, lalata asibitoci da kuma mamaye wasu 'yan uwa ba bisa ka'ida ba.
Har ila yau, sakatariyar harkokin wajen Burtaniya Liz Truss ta ce:
"Takunkumin na yau ya sake nuna cewa 'yan kama karya da masu cika aljihu da kudin kasa ba su da wani matsayi a cikin tattalin arzikinmu ko kuma al'ummarmu. Kusancinsu da Putin ke nuna suna da hannu wajen ta'addancin nasa.
"Jinin al'ummar Ukraine na hannunsu, ya kamata su rataye kawunansu saboda kunya.
"Goyon bayanmu ga Ukraine ba zai kassara ba. Ba za mu tsaya wata-wata ba a wannan aiki na kara matsi kan gwamnatin Putin da kuma kassara kudaden na'urar yakinsa na zalunci ba."
Yakin Rasha Da Ukraine: Gwamnatin Putin Ta Lissafo Jerin Kasashen Da Bata 'Ga-Maciji' Da Su
A wani labarin, Rasha a ranar Litinin 7 ga watan Maris ta wallafa jerin sunayen kasashen kasar waje da ta dauke su a matsayin wadanda ta 'ki jini', Newsweek ta rahoto.
Rasha ta ce daga yanzu ana bukatar izini na musamman daga gwamnati kafin a yi ko wane irin kasuwanci ne da kasashen, a wani martanin da ta yi na takunkumin karya tattalin arziki da aka saka mata kan kutsa wa cikin Ukraine.
Kasashe da yankunan da Rasha ta dauka a matsayin makiyanta sun hada da Australia, Albania, Andorra, the United Kingdom, Anguilla, British Virgin Islands, Gibraltar, Iceland, Canada, Liechtenstein, Micronesia, Monaco, New Zealand, Norway, da Taiwan.
Asali: Legit.ng