Yakin Rasha Da Ukraine: Gwamnatin Putin Ta Lissafo Jerin Kasashen Da Bata 'Ga-Maciji' Da Su

Yakin Rasha Da Ukraine: Gwamnatin Putin Ta Lissafo Jerin Kasashen Da Bata 'Ga-Maciji' Da Su

  • Gwamnatin Rasha ta saki jerin sunayen kasashe da yankunan da ba ta ga maciji da su yayin da ta afka wa Ukraine da yaki
  • Saboda takunkumin tattalin arziki da aka saka mata, tattalin arzikin kasar Rasha ya fara shiga matsala saboda kaurace mata da aka yi
  • Rasha ta kutsa cikin kasar Ukraine a watan Fabrairu, amma dakarunta sun samu tsaiko saboda matsalar zirga-zirga da turjiyya daga sojojin Ukraine

Moscow - Rasha a ranar Litinin 7 ga watan Maris ta wallafa jerin sunayen kasashen kasar waje da ta dauke su a matsayin wadanda ta 'ki jini', Newsweek ta rahoto.

Rasha ta ce daga yanzu ana bukatar izini na musamman daga gwamnati kafin a yi ko wane irin kasuwanci ne da kasashen, a wani martanin da ta yi na takunkumin karya tattalin arziki da aka saka mata kan kutsa wa cikin Ukraine.

Kara karanta wannan

Ta kare wa Putin: Shugaban Rasha na neman sojojin da za su taya shi yaki da Ukraine

Yakin Rasha Da Ukraine: Gwamnatin Putin Ta Lissafo Jerin Kasashen Da Bata 'Ga-Maciji' Da Su
Ukraine: Gwamnatin Putin Ta Lissafo Jerin Kasashen Da Bata 'Ga-Maciji' Da Su. Photo credit: Ramil Sitdikov/Sputnik/AFP
Asali: Getty Images

Jerin kasashen da Rasha ta ce bata ga-maciji da su

Kasashe da yankunan da Rasha ta dauka a matsayin makiyanta sun hada da Australia, Albania, Andorra, the United Kingdom, Anguilla, British Virgin Islands, Gibraltar, Iceland, Canada, Liechtenstein, Micronesia, Monaco, New Zealand, Norway, da Taiwan.

Saura sun hada da Jamhuriyar Korea, San Marino, North Macedonia, Singapore, Amurka, Taiwan, Montenegro, Switzerland, da Japan.

Kasashen da ke jerin an dauke su a matsayin makiya ne saboda daukan mataki na rashin kirki ga Rasha, kamfanoninta da al'ummar kasar.

Sai an nemi izini daga gwamnati kafin a yi kasuwanci da kasashen, Gwamnatin Rasha

Ana bukatar izini daga wata hukuma ta Gwamnatin Rasha - Hukumar Kula da Hannun Jari na Kasashen Waje, wacce aka kafa a 2008 don saka ido kan hannun jari na kasashen waje ta sanar.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Saudiyya ta dage wasu dokokin Korona yayin da Ramadana ke karatowa

Sanarwar ta ce kamfanoni, yan kasuwa da mazauna Rasha za su rika biyan bashi da ake binsu na kasashen wajen ne ta hanyar amfani da rubles.

Wannan dokar ya shafi duk wata hada-hadar kudi da za a yi da ya kai rubles miliyan 10.

Sanarwar ta kuma ce hukumar na gwamnatin Rasha da ke kula da saka hannun jari ce za ta rika bada izinin yin kasuwanci da yan kasar Rasha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel