Da dumi-dumi: Sarauniyar Ingila ta kamu da cutar korona

Da dumi-dumi: Sarauniyar Ingila ta kamu da cutar korona

  • Fadar masarautar Buckingham ta sanar da cewar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, ta harbu da cutar korona
  • Kamar yadda fadar ta sanar a yau Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, sarauniyar za ta ci gaba da gudanar da harkoki sama-sama
  • Ta kuma bayyana cewar Elizabeth II za ta ci gaba da samun kulawar likitoci tare da bin ka'idojin da suka dace

Labari da muke samu a yanzu ya nuna cewa Sarauniyar Ingila, Elizabeth II mai shekaru 95 a duniya, ta kamu da annobar korona, rahotonb Aljazeera.

Fadar masarautar Buckingham ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, jaridar The Cable ta rahoto.

Da dumi-dumi: Sarauniyar Ingila ta kamu da cutar korona
Sarauniyar Ingila ta kamu da cutar korona Hoto: nytimes.com
Asali: UGC

A cewar fadar, sarauniyar na fama da alamun sanyi amma kuma za ta ci gaba da gudanar da harkoki kadan-kadan a Windsor a mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Cibiyar horar da lauyoyi ta kama da wuta, an zarce da mutum 5 asibiti

Fadar ta ce:

“Za ta ci gaba da samun kulawar likitoci sannan za ta bi dukkan matakan da suka dace.”

Sarauniyar ta hadu da babban danta kuma yarima mai jiran gado, Yarima Charles wanda ya kamu da korona a makon da ya gabata.

Shekaru 70 kan karagar mulki: Sarauniyar Ingila ta kafa tarihin da aka jima ba’a gani ba

A gefe guda, mun kawo a baya cewa a ranar 6 ga watan Fabrairun bana ne Sarauniya Elizabeth II ta cika shekaru 70 a kan karagar mulkin Burtaniya.

Jaridar New York Times ta ba da rahoton cewa wannan ci gaba ya sanya sarauniyar cikin rukunin da ba a cika gani ba a tarihi, inda tarihi ya rubuta cewa, wasu sarakuna uku ne kawai aka san sun yi mulki sama da shekaru 70.

Kara karanta wannan

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

Kafar labarai ta CNN ta kara da cewa Elizabeth II, mai shekaru 95, ta zama sarauniyar Burtaniya ne bayan rasuwar mahaifinta King George VI a ranar 6 ga Fabrairu, 1952, yayin da take kasar Kenya a wani rangadi na kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel