A karon farko, an gano mugun irin Covid-19, SARS-Cov-2 a Najeriya

A karon farko, an gano mugun irin Covid-19, SARS-Cov-2 a Najeriya

  • Hukumar NCDC ta tabbatar da gano sabon nau'in cutar korona mai suna SARS-Cov-2
  • An gano nau'in cutar a jikin wani matafiyi da ya shigo daga kasar waje a jihar Delta
  • An gano cewa sabon nau'in cutar koronan yana da alaka da cigaban yaduwar cutar

Hukumar kula da dakile cutuka masu yaduwa, NCDC, ta ce ta gano mugun nau'in cutar korona mai suna SARS-Cov-2 a jihar Delta dake Najeriya.

A wata takardar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis da dare a Facebook, ta ce nau'in da aka sani da B.1.17.2 an gano shi ne a jikin wani matafiyi da ya shigo Najeriya.

KU KARANTA: Mun aike 'yan bindiga masu yawa ga Mahaliccinsu, COAS Farouk Yahaya

A karon farko, an gano mugun irin Covid-19, SARS-Cov-2 a Najeriya
A karon farko, an gano mugun irin Covid-19, SARS-Cov-2 a Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ta fasu: Magu ya hana bincikar Fintiri da wasu tsoffin gwamnoni 3, Kwamitin Salami

Ta ce bayan gwajin da aka yi wa dukkan matafiya daga kasashen waje da suka shigo kasar nan, an gano cewa akwai sabon nau'in cutar korona a dakin gwajin NCDC dake Abuja.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta ce nau'in cutar korona da aka gano a jihar Delta za ta iya cigaba da yaduwa a kasar nan.

An gano nau'in kwayar cutar a sama da kasashe 90 kuma ana tsammanin zai yadu zuwa wasu kasashen nan gaba.

NCDC ta ce nau'in cutar tana da alaka da abinda yasa cutar korona ke cigaba da karuwa a duniya amma a kasashen da tsohon nau'in yake.

Ana cigaba da bincike tare da kokarin gano ko riga-kafin da magungunan tsohon nau'in korona zasu yi mata.

A wata takarda da NCDC ta fitar, ta ce tana aiki da hukumar binciken magunguna ta NIMR, ACEGID da sauran dakunan bincike a kasar nan wurin gano yanayin cutar.

A wani labari na daban, mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta ce ita ba 'yar siyasa bace amma tana bin ka'idojin aikinta ne a komai.

Ta sanar da hakan ne yayin jawabin farko yayin da ake tantanceta a matsayin kwamishinan kasa ta INEC a majalisar dattawa, Daily Trust ta ruwaito.

Ta ce, "Bani da jinin bangaranci. Na ga korafe-korafe daban-daban kan zabena da aka yi ba daga PDP ba kadai, har da wasu 'yan APC."

Asali: Legit.ng

Online view pixel