Pandora Papers: An sake bankaɗo manyan kamfanonin gwamnan APC na 3 na ƙasar waje
- Takardun Pandora na kungiyar bincike na ‘yan jaridun duniya, ICIJ ta bankado gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, gwamna na 3 a jam’iyyar APC
- Kamar yadda takardun su ka fallasa, Abiodun darekta ne na a kalla kamfanoni 2 da ke kasashen ketare kuma ya na aiki da asusun bankuna na kasar waje
- Kamfanonin na shi su na tsibirin British Virgin ne kuma ko lokacin da zai bayyana kadarorin da ya mallaka, be lissafo sunan kamfani ko guda daya ba daga cikin su
Hukumar bincike ta ‘yan jaridun duniya ta ICIJ ta yi bincike wanda takardun Pandora su ka fallasa gwamna jihar Ogun, Dapo Abiodun, gwamna na 3 karkashin jam’iyyar APC.
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, dama an bankado asirin wasu gwamnoni 2 na daban, Gwamna Atiku Bagudo na jihar Kebbi da Gboyega Oyetola na jihar Osun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Takardun sun nuna yadda Abiodun ne darekta na akalla wasu kamfanoni 2 yayin da ya ke amfani da asusun kasar waje.
Kamfanonin a tsibirin British Virgin su ke
Kamar yadda takardun su ka bayyana:
“Mun gano yadda ya ki bayyana kamfanonin a lokacin da ya ke nuna kadarorin sa ga Code of Conduct Bureau.”
“An gano takardun ne yayin bincike akan kamfanonin da wadanda su ka mallake su. Mafi yawan su hamshakan ‘yan kasuwa ne, ‘yan siyasa da marasa gaskiyar da su ke so su boye harkokin kudaden su.”
“Binciken hadin guiwar da aka yi shekaru 2 ana yi ya fallasa cewa sirrin dukiyar na akalla manyan shugabannin duniya 40 ne da su ke kan kujerun su ko kuma wadanda su ka sauka, sannan manyan ma’aikatan gwamnati sun kai 330 na kasashe 91.”
Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC
“Takardar ta bayyana cewa Abiodun shi ne darekta kuma mai kamfanin Marlowes Trading Corporation, kamfanin da ya ke aiki karkashin dokokin tsibirin British Virgin.”
“Har ila yau, gwamnan be bayyana kamfanin sa na man fetur ba, na Heyden Petroleum Limited da dayan kamfanin sa na BVI wanda ya yi wa rijista a kasashen waje.”
Yayin da Abiodun ya so kafa kamfanin a kasar waje, an samu rahotanni akan yadda ya yi hayar SFM Corporate Service da ke Dubai don neman shawarwari.
SFM Corporate Service sun kware ne wurin kafa kamfanoni a kasashen waje, bude asusun bankuna da kuma sauran ayyuka makamantan hakan.
A shekarar 2015 aka kafa kamfanin
Kamar yadda takardar ta nuna:
“SFM Corporate Service ta yi hayar Aleman, Cordero, Galindo & Lee (alcogal), don samar da kamfanin kasuwanci na Marlowes Corporation, kamfanin Abiodun.”
“Bayan kokarin SFM da Alcogal, aka kafa kamfanonin kasashen wajen na sa dake tsibirin British Virgin a ranar 12 ga watan Janairun 2015.”
“Mr Abiodun ya zama darekta kuma mai kamfanin. Sannan an ba shi takardun duk kamfanin.”
“A watan Maris na 2015 ne aka kammala rijistar kamfanin, daga nan ne Alcogal su ka tura sababbin takardun kamfanin zuwa ga SFM Corporate Service dake Dubai, daular larabawa.”
Baya ga Marlowes, takardun sun nuna cewa Abiodun ne mai kamfanin Heyden Petroleum Limited, wanda sunan sa daya da wani kamfanin sa na Najeriya.”
Ya kafa kamfanin ne a shekarar 2001
Takardun na ranar 21 ga watan Maris din 2016 sun nuna cewa gwamnan ne mai kamfanin Heyden BVI shi daya.
Saidai a takardar wacce aka gabatar wa SFM Corporate Services, Abiodun ya yanke shawarar barin wani Okechukwu Chikezie Nzelum damar ci gaba da aiwatar da duk wasu harkokin kamfanin.
Gwamnan be ba Chikezeim damar amfani da kamfanin wurin aiwatar da wasu harkokin kasuwanci ba.
Premium Times ta bayyana yadda gwamna Abiodun ya ki bayar da amsar sakonni da aka tura ma sa ta wayar sa da shafin sa na yanar gizo dangane da wannan lamarin.
Har sakataren watsa labaran gwamnan, Kunle Somorin ma ya ki bayar da amsar sakon da aka tura ma sa dangane da lamarin kamar yadda Premium Times ta tabbatar.
Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari
A wani rahoton, ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.
Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.
Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.
Asali: Legit.ng