Mutane miliyan 25 na iya rasa abin yi saboda tashin Dala da wahalar kayan abinci inji PAN
- Kungiyar PAN tace ana iya fuskantar matsala wajen harkar noman kaji a Najeriya
- Shugaban PAN, Ezekiel Ibrahim yace miliyoyin manoma kaji za su iya rasa aikin yi
- Ibrahim ya bayyana wannan a ranar bikin ‘kwai’ na Duniya, ya yi kira ga gwamnati
Abuja - Kungiyar PAN ta masu kiwon kaji na kasa, ta ce mutane miliyan 25 na iya rasa hanyar samun abincin su saboda kalubalen da ake fuskanta a yau.
Jaridar The Cable ce ta rahoto shugaban kungiyar PAN na kasa, Ezekiel Ibrahim ya na wannan bayani a ranar da ake bikin tuna wa da kwai a fadin Duniya.
Da yake jawabi a babban birnin tarayya Abuja, Ezekiel Ibrahim yace mutane za su rasa aikin yi.
Wani Darekta Janar na kungiyar PAN, Onallo Akpa ne ya wakilci Ibrahim a wajen wannan biki na musamman da aka yi ranar Asabar, 9 ga watan Oktoba, 2021.
An rahoto Akpa yace muddin ba a dauki matakin gaggawa ba, za a gamu da cikas wajen kiwon kaji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin shugaban kungiyar PAN
“Harkar kiwon kaji yana daf da ya sukurkuce, kuma idan hakan ta faru, akwai matsalolin da za su shafi mutane da dama.”
“Muna fuskantar karancin masara da tsadar kudin kasar waje. Masu kiwo a ketare suna jira, su ga kaji sun kife a Najeriya.”
“Idan hakan ta faru, kasuwa ce a gare su domin mu na da dinbin mutanen da za su ci ciniki.”
“Muna neman gwamnati ta duba wasu tsare-tsarenta. Muna bukatar gudumuwar gwamnati domin mu cin ma nasara.”
“Idan babu gudumuwarsu, duk kudin da aka narka ba zai haifar da riba ba.” - Ezekiel Ibrahim.
Inda matsalar take
Ana hasashen cewa karancin masara da waken suya da ake amfani da su wajen hada abincin kaji za su kawo cikas, game da tashin da irin Dalar Amurka ta yi.
Babu labarin Sarkin Bungudu
A ranar Talatar nan aka ji cewa ‘Yan bindiga su na ta cigaba da tsare Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru bayan sun karbi miliyoyin kudin fansa a hannun danginsa.
Wani ‘Danuwansa yace tun da su ka biya kudin fansa, babu wanda ya kara magana da Sarkin. Yanzu ana maganar kwana 30 kenan da aka yi gaba da Mai martaba.
Asali: Legit.ng