Ahmad Yusuf
11619 articles published since 01 Mar 2021
11619 articles published since 01 Mar 2021
Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia ya sanar da sa dokar zaman gida a ƙaramar hukumar Ukum da kewaye biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga a yankin.
Majalisar dattijan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta sauya salon tunkarar ƴan tada kayar baya domin magance hare-hare irin wanda aka kai Gwoza a Borno.
Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hajiya Salamatu Ahmed a matsayin shugabar hukumar bada lamunin gidaje ta tarayya FGSHLB.
Majalisar wakilan tarayya ta fara karatun farko kan kudirin kirkiro sabuwar jihar Etiti a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya domin jihohin yankin su zama 6.
Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bayar da gudummuwar N5bn domin karisa ginin sasanin NYSC, ya kuma yi alƙawarin ɗaukar likitoci daga cikin ƴan bautar kasa.
Shugaban majalisar dokokin jihar Imo, Chike Olemgbe ya sanar da dakatar da ƴan majalisa 4 bisa zarginsu da kulla yadda za su tunuke shi daga mukaminsa.
Dakarun sojojin Najeriya sun damƙe wasu mata masu tallar zuma a bakin titi waɗanda aka gano suna taimakawa ƴan bindiga da bayanan sirri a jihar Kaduna.
Dillalan man fetur a Najeriya sun nuna fargabar cewa da yiwuwar ba za a samu saukin da ake tsammani a fetur ba idan matatar Ɗangote ta shigo da nata kayan kasuwa.
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kebbi ta tabbatar da rasuwar Hajiya Maryamu daga ƙaramar hukumar Maiyama, ta rasu ne a asibitin Sarki Abdul'aziz da ke Makkah.
Ahmad Yusuf
Samu kari