Ahmad Yusuf
11466 articles published since 01 Mar 2021
11466 articles published since 01 Mar 2021
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce tsoro da rashin kwarin gwiwa ne kadai zai aa mutum ya bar jam'iyyar PDP, ya ce taron da aka shirya aIbadan na nan daram.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci Majalisar Dokokin Jihar Benuwai, ta sake nazari kan batun bashin da Gwamna Alia zai karbo har Naira biliyan 100.
Rahotanni sun nuna cewa ba gwamnan Enugu kadai zai koma APC a mako mai zuwa ba, Gwamna Douye Diri na Bayelsa da wasu gwamna sun shirya barin tsagin adawa.
Yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki yau Juma'a, an ga al'ummar Falasdinu sun fara kokarim komawa gidajensu da ke Arewacin Gaza duk da an lalata su.
Tsohon Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Agboola Ayoola ya mika wasikar ficewarsa daga jam'iyyar PDP a jihar Oyo, ya ce zai canza akalar siyasa.
Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya amince zai sa baki kan batun jagoran IPOB da ke daure, Nnamdi Kanu.
Jam'iyyar APC ta hana yan siyasa biyu shiga zaben fidda gwanin da zata shirya domin tsaida dan takarar gwamnan jihar Ekiti a zaben da za a yi a shekarar 2026.
Kwamitin rikon kwarya da APC ta kafa a jihar Enugu ya tabbatar da cewa Gwamna Peter Mbah da mukarrabansa za su dawo jam'iyya mai mulkin Najeriya a makon gobe.
Mayakan kungiyar ta'addanci ta ISPWA sun kai hari wani sasanin rundunar sojin Najeriya a Borno da sanyin safiyar ranar Juma'a,ana fargabar rasa rayuka.
Ahmad Yusuf
Samu kari