Jama'ar wani gida a Kaduna sun gudu sun bar gidansu bayan dan uwansu da ya dawo daga Legas ya fara zazzabi da mura

Jama'ar wani gida a Kaduna sun gudu sun bar gidansu bayan dan uwansu da ya dawo daga Legas ya fara zazzabi da mura

Wasu mazauna unguwar Kurmi da ke yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun shiga rudani bayan wani matashi da ya dawo daga Legas ya fara nuna alamun masassara.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa jama'ar unguwar sun kara gigita bayan mazauna gidan da matashin yake sun gudu bayan ya fara nuna alamun masassara kwatankwacin ta masu dauke da cutar covid-19 tun bayan dawowarsa daga jihar Legas a ranar 5 ga watan Afrilu.

Liman Hamisu, dagacin garin Kurmin Kaduna, ya shaidawa NAN cewa 'yan uwan mutumin sun tsere daga gidansu bisa tsoron cewar ko ya kamu da kwayar cutar coronavirus.

"Mutanen gidan sun gudu sun barshi bayan ya fara amai da zazzabi mai zafi.

"Bayan guduwar mutanen gidan, sai jama'ar unguwa suka shiga halin damuwa bisa tunanin cewa ko ya gudo daga cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da ke Legas," a cewar Hamisu.

A cewarsa, mutanen unguwa sun kira cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) da wakilan jami'an lafiya daga karamar hukumar Igabi, kuma dukkansu sun tabbatar da cewa alamun rashin lafiyarsa ba su yi kama da na mai dauke da cutar covid-19 ba.

Jama'ar wani gida a Kaduna sun gudu sun bar gidansu bayan da uwansu da ya dawo Legas ya fara zazzabi da mura
Jama'ar wani gida a Kaduna sun gudu sun bar gidansu bayan da uwansu da ya dawo Legas ya fara zazzabi da mura
Asali: Twitter

"Bayan mun addabi hukumar NCDC da kira, ta turo wakili zuwa garinmu domin ganin halin da matashin ya ke ciki.

DUBA WANNAN: Yadda za mu cigaba da ciyar da dalibai duk da an rufe makarantu - Ministar jin dadi da walwala

"Kazalika, wani jami'in hukumar lafiya daga karamar Igabi ya tabbatar da cewa mutumin ba ya dauke da kwayar cutar covid-19," a cewarsa.

Dagachin ya roki 'yan uwan mutanen da su daure su dawo gida don yanzu an tabbatar da cewa dan uwansu ba ya dauke da kwayar cutar covid-19.

Ya ce dawowarsu ce kadai za ta kwantar da hankalin mutanen unguwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel